Hukumar Hisbah da ke da alhakin dabbaka kyawawan dabi’u bisa koyawar addinin Islama a Jihar Kano, ta haramta amfani da mutum-mutumi wajen tallata haja a manyan shaguna da sauran wuraren sayar da kayayyaki a Jihar.
Kwamandan hukumar, Sheikh Harun Ibn-Sina ne ya bayyana haka a wata tattaunawarsa da Aminiya, ranar Laraba.
- Tsohon Sakataren Tsaron Amurka Donald Rumsfeld ya mutu
- Lasisin tuka Adaidata Sahu ya koma N100,000 —KAROTA
Ibn-Sina ya ce amfani da mutum-mutumin da tailoli da wasu manyan shaguna ke yi ya sabawa koyarwar addinin musulunci kasancewar ba su da wani bambanci da gumaka.
Sanarwar ta ce “Hisbah ta haramta amfani da mutum-mutumi a bainar jama’a da sauran wurare.
“Tsarin addinin musulunci shi ne ya koyar da kyawawan dabi’u a tsakanin al’umma.
Kazalika, ya ce hukumar za ta shirya taron gangamin wayar da kan al’umma kan illar amfani da mutum-mutumin, sannan kuma za ta sa kafar wando daya da duk wanda suka yi kunnen uwar shegu da dokar.
A cewarsa taron gangamin zai mayar da hankali kan manyan wurare da suke amfani da shi, don yi musu bita kan illar da ke tattare da hakan.
“Mun kasa Kano zuwa gida biyar don bi daki-daki wajen wayar da kan mutane game da dokar hana amfani da mutum-mutumin a fadin jihar.”