✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Hisbah ta cafke mutum 78 kan zargin hada auren jinsi a Kano

Ana zargin matasan maza da mata da kitsa auren jinsi a tsakaninsu.

Hukumar Hisbah a Jihar Kano ta cafke wasu mutum 78 maza da mata bisa zargin hada auren jinsi a tsakaninsu.

Hukumar ta cafke su ne a unguwar Nassarawa GRA a wani gida da ya yi kaurin suna wajen aikata masha’a da ake kira ‘White House’.

Bayanai sun ce Hisban ta kai samame gidan ne riski maza da mata cakude ana casu kari a kan kororon roba da suka jibge a na ta shagali.

Tuni Hisbah ta cafke mutum 78 yayin da wasu kuma suke tsere, amma hukumar a yanzu haka gudanar da bincike.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, matasan wadanda suka musanta zargin, sun ce suna casun ne a matsayin bikin murnar zagayowar ranar haihuwar daya daga cikinsu.

Ko a shekarar da ta gabata sai da hukumar Hisbah ta cafke wasu matasa maza da ake zargi da yunkurin daura auren jinsi, wanda shi ma a wancan lokaci suka musanta.