✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hisba ta kama karuwai 7 a Jigawa

Rundunar Hisba a Jihar Jigawa ta kai wani samame wani gida da ke daf da kasuwar Shuwarin a Karamar Hukumar Kiyawa tnda ta samu nasarar…

Rundunar Hisba a Jihar Jigawa ta kai wani samame wani gida da ke daf da kasuwar Shuwarin a Karamar Hukumar Kiyawa tnda ta samu nasarar cafke wadansu karuwai bakwai a gidan da suke yin sana’ar karuwanci.

Kwamandan Hisba na Jihar Jigawa Malam Ibrahim Dahiru Garki ya tabbatar da faruwar wannan lamari.

Ya ce an kama karuwan ne a lokacin da suke tsakiyar yin sharholiya a gidan wata magajiya Maryam Hassan.

A jawabin Maryam Hassan ta ce su ba karuwai ba ne suna sana’ar sayar da tuwo ne amma saboda rashin gata hukumar ta damke su a matsayin karuwai.

Ta ce sun sha samun rahoton a kan yadda rundunar take kama masu yin zina a Masallaci da ’yan luwadi a sassan yankin amma ba a yi musu komai, haka ake sakinsu, amma su da yake ba su da gata yanzu an kama su a matsayin karuwai.

Ta ce a Shuwarin akwai gidajen karuwai masu yawa amma abin mamaki sai hukumar ta tsallake su ta fado gidansu kuma ta ce ta kama su a matsayin karuwai.

Kwamnandan Hisban a nasa martanin ya ce ba su da masaniyar akwai wani gidan karuwai in ban da wannan, amma da yake yanzu sun samu labari zau su ci gaba da kai samame sauran gidajen karuwan.

A wani labari makamancin wannan, Hukumar Hisba ta kai wani samame Karamar Hukumar Ringim inda ta kama wani matasi yana shan mangwaro da tsakar rana.

Matashin mai suna Ibrahim Isma’il, hukumar ta kama shi ne a tsakiyar kasuwar Ringim yana shan mangwaro da rana tsaka alhali ana yin azumin Ramadan.

An dai gurfanar da matashin a gaban kotun shari’ar Musulunci da ke Ringim inda aka zartar masa da hukuncin bulala 40 a bainar jama’a.

Kotun ta ce ta yi amfani ne da sashi na 370 na final kod a tsarin shari’ar Musulunci na Jihar Jigawa.

Mai Shari’a Safiyanu Ya’u Kiri ya ce an yi wa matashin bulala 40 ne a bainar jama’a don ya zama darasi ga masu neman aikata laifi irin nasa.