Dabara ta 3: Ki dubi sakamakon rashin yin biyayya: Kamar yadda kyautata wa maigida da girmamawa da darajtawa sakamakonsu yake gidan Aljannar ni’ima, haka nan munana zamantakewa ga maigida na iya jefa uwargida ga halaka ranar gobe kiyama. Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya bayyana cewa mafi yawan ’yan wuta mata ne saboda rashin godiyarsu ga mazansu. A wani kaulin kuma ya ce da wata Sahabiya: “Ki kula sosai da yadda kika mu’amalance shi domin shi ne Aljannarki kuma shi ne wutarki.”
Haka nan duk matar da mijinta ya yi fushi da ita Wanda ke sama (Subhanahu Wa Ta’ala) Zai yi fushi da ita har sai mijin ya daina fushi da ita, kuma duk ibadunta ba a amsarsu har sai mijin ya daina fushi da ita.
Lallai akwai hadurra da yawa ga macen da take munana zamantakewa ga mijinta har mutuwa ta riske ta a wannan hali. Don haka uwargida sai ki auna ki gani, wanne ya fi miki muhimmanci; ki a je duk wani jiji-da-kanki da fadin rai, ki yi fatali da duk wani abu da ke kange ki daga yin ladabi da girmama maigidanki don ki tseratar da kanki daga azabar wutar Jahannama don ki dace da Aljannar Ni’ima. Lallai in kika duba sakamakon rashin girmama maigida, to duk wani abu da za ki yi don kubuta daga gare shi kadan ne, ga shi kuma girmama maigida na janyo alherai masu yawa tun a nan duniya mafi alfanu a cikinsu shi ne za ki samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a gidan aurenki.
Dabara ta 4: Ki fahimci matsayin mijinki: Kamar yadda Hadisin da ke sama ya bayyana, maigida shi ne Aljannar matarsa ko kuma wutarta, don haka uwargida kada ki dubi isa ko rashin isar maigidanki a idonki, kada ki dubi wadatarsa ko akasin haka, kada ki dubi kyautatawarsa ko rashin kyautatawa da sauran duk wani abin awo da zai shigo zuciyarki ki ce da su ne za ki auna ki rika ba shi girma daidai da haka. Ki dubi matsayinsa na shi ne kofar Aljannarki kuma hanyar kubutarki daga wuta, to ai kuwa wannan ba abin yin sakaci ba ne. Ya kamata ki yi dukan sadaukarwa kuma ki ba da dukan karfinki da dukan dagewarki kuma ki nace da hakuri har iya karshen rayuwarki ki kasance a kan haka.
Ki sani ya ke uwargida! Cewa maigidanki yana da matukar girma da matsayi a wajenki fiye da na zamansa mijinki kadai; Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) yana cewa da zan umarci wani ya durkusa ga wani don girmamawa da na umarci mace ta durkusa ga mijinta don girman matsayinsa. Haka nan Uwar Muminai A’isha (Radiyallahu Anha) ta yi wannan kira ga mata:
“Ya ku mata! In da kun san girman hakkin da mazanku ke da shi a kanku, lallai da kowaccenku ta share dattin tafin kafar mijinta da fuskarta!”
Dabara ta biyar: Koyi da magabata: Wani abu da zai kara wa uwargida kwarin gwiwa wajen dada dagewa ga girmama maigidanta shi ne yin koyi da nagartattun mata daga cikin magabata Radiyallahu Anhunna. Lallai sun kasance masu kyautatawa da girmama mazansu da yin hakuri da su.
Misali na 1: Uwar Muminai A’isha Radiyallahu Anha, saboda yadda take darajtawa da girmama maigidanta Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ko fushi ba ta bayyana masa a fuskarta balle a furuci da mu’amala, a yanayin rantsuwarta kadai Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam)yake gane tana fushi da shi, maimakon ta ce ‘Na rantse da Ubangijin Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam) ‘yadda ta saba, in tana fushi da shi sai ta ce ‘Na rantse da Ubangijin Ibrahim (Alaihis Salam).’ Don haka danne fushi da rashin bayyana shi ga maigida abu ne da kowace mace ya dace ta dage masa don dacewa da alheran gidan Lahira, domin duk wanda yake cikin fushi hankalinsa yakan dan baci, duk abin da za ki fada ga maigida lokacin da kike cikin fushi zai zama ko dai na raini ko na batanci da bakanta rai, don haka rashin yin ya fi zama alheri. Abu ne mai wuya kam, kuma komai dagewa wata ran ana iya samun bacin rana, wannan ba komai, abin da ba a so kada hakan ya zama dabi’a a ce kullum ko duk mako ko duk wata, wannan zai iya zama sanadiyyar hallaka ga uwargida. Da fatan Allah Ya sa mu dace, amin.
Sai mako na gaba, insha Allah. Da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a koyaushe, amin.