Hikima ta 4: Girmamawa da darajta maigida: ci gaba…
5. Yana daga cikin girmamawa ga maigida rashin katsalanda da tsoma masa baki cikin harkokinsa wadanda ba su shafi dangatakarsa da uwargida ba sai dai in shi ne ya nemi jin ra’ayinta. Haka ba shi shawara game da wata harka ba tare da ya nemi jin ta bakinki ba.
A kiyaye…
*Girmama maigida a zahiri amma a badini can cikin zuciyarki ba ki yi masa wannan daukar darajar da wannan ganin girman, bai da wani alfanu kuma ba abin da zai harfar miki sai tsana da hantara daga zuciyar maigida, domin komai yadda kika kai ga iya boye sirrin da ke zuciyarki, a hankali maigida zai gane cewa aikinki bai kai zuci ba. Haka kuma in kika boye girmamawa da darajtawar da kike yi wa maigidanki ba ki bayyanar da su cikin huldodinki da shi, to za ki samu matsala ta bangaren bukatocinki na yau da kullum, zai rika hana ki bukatunki koda kuwa ba su fi karfinsa ba musamman mafi soyuwa gare ki kamar yadda kika hana masa girmamawa da darajtawa. Don haka uwargida a kula kuma a kiyaye, dole sai an cakuda duka biyun sannan ake cin moriyarsu.
Dabarun kwarewa wajen girmama maigida
Assalamu alaikum duniyar ma’aurata. Gaskiya kun soso mini inda yake mini kaikayi domin ina jin wahalar bayyana girmamawa ga maigida, ina son sa ina kishinsa, ina son in ga ci gabansa da karuwarsa, amma kuma ba na iya yi masa wannan girmamawar da na ga wadansu mata na yi wa mazansu. A kan haka muna yawan samun sabani da shi. Ban sani ba ko don na fi shi zurfin ilimi, na fi shi yawan albashi, wayewa da sauransu shi ya sa abin ke yi mini wuya? Kafin in aure shi ban zaci zan samu wannan matsalar ba amma abubuwa da yawa game da aure sai ka shiga kake fahimtarsu. Ko cewa ya yi in kawo masa ruwa cikin kunar rai nake zuwa, sai inji me ya sa ba zai tashi ya dauko da kansa ba? Sannan ni irin gidanmu mahaifinmu har girki yake yi, bai tsayawa ya ce komai sai mahaifiyarmu ta yi masa. Ina son in gyara don mu daina yawan fadace-fadace a gaban yara, don Allah ku ba ni dabarun yadda zan yi don in samu saukin girmamawa ga maigida, domin na san akwai mata da yawa irina.
Daga Hajiya Rabi Maman Twins…
Dabara ta 1: Ki dubi girman wanda Ya ce ki yi biyayya: Uwargida ki fahimci cewa girmamawa da darajta maigida umarnin Allah (Subhanahu Wa Ta’ala) ne, haka nan umarnin Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ne, don haka kada ki yi dubi ga matsayin mijinki a wajenki da darajarsa a zuciyarki ya zama da shi za ki auna irin girmamawa da darajtawar da za ki yi masa, a’a ki yi dubi zuwa ga girman umarnin Allah da darajar aiki da Sunnar Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam). Wadannan su zama abin dogaro gare ki, tudun dafawa wajen dagewa da girmama maigida, darajta shi da yi masa ladabi da biyayya. Kullum ki rika tunowa ibada kike, bautar Allah kike yi, aiki da umarnin Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) kike yi; wannan zai taimaka miki wajen ruguje duk wani jiji-da-kai da bunkasar zuciya da ka iya katange ki daga yin ladabi, biyayya da bayyanar da girmamawa ga maigidanki. Wato girmamawar da kike yi ga maigida asalinta ladabi ne da kuma girmama umarnin Allah Madaukakin Sarki.
Dabara ta 2: Ki dubi sakamakon biyayya: Sannan ki yi dubi zuwa ga sakamakon yin biyayya da girmama maigida, babban sakamakon da babu kamarsa, Aljanna madaukakiya gidan ni’ima da jin dadi marar yankewa. Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce duk macen da ta yi sallolin farilla biyar, ta azumci watan Ramadan, ta tsare mutuncinta, ta yi ladabi ga maigidanta, za a ce da ita shiga Aljanna ta duk kofar da kike so. Don haka yin ladabi ga miji yana daga cikin shika-shikan shiga Aljannarki wanda in ba shi to akwai matsalar kaiwa ga mukamin shiga Aljanna.
Haka kuma Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce mace a gidan mijinta tana kula da yaranta da gidanta tana da matsayi da kuma ladan jarumi a fagen yaki don daukaka kalmar Allah (Subhanahu Wa Ta’ala). Don haka ki dubi girman matsayinki ba na wasa ba ne, ki dage masa ki rike shi da kyau kuma ki yi hakuri da dauriya a kan duk abin da zai same ki a filin dagar gidan aurenki, ki rika hango babban ladan da ke jiranki sai ki ga wannan ai ba komai ba ne.
Sai mako na gaba Insha Allah, da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a kodayaushe, amin.