Bakuwarmu ta wannan mako, ita ce Shugabar Mata ta Kungiyar Gizago ta Najeriya, Hajiya A’ishatu Lawan. A sakonta ga daukacin Gizagawa, tana cewa:
“Assalamu alaikum! Ina yi wa daukacin Gizagawan Zumunci fatar alheri. Allah Ya kara taimakon wannan kungiya mai albarka, amin. Allah Ya kara dankon zumunci, Ya ba mu sa’ar cimma burinmu. Amin Ya Rabbi. Wassalamu alaikum warahmatullah wa barakatuhu!
***
A labarin jajantawa kuwa, muna sanar da cewa Bagizage Abubakar Mahmud (08165757385) daga Jihar Gombe, Allah Ya yi wa dansa rasuwa. Allah Ya jikansa da rahma, amin!