✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hidima ga al’umma ce ta sa na samu sarauta a Kurmi – Sarkin Hausawan Alimoso

Ko za mu fara da jin tarihinka a takaice? Sunana Alhaji Ahmad Haruna Kuraja Sarkin, Hausawan Alimosho kuma Shugaban Majalisar Sarakunan Hausawa na wannan yanki.…

Ko za mu fara da jin tarihinka a takaice?

Sunana Alhaji Ahmad Haruna Kuraja Sarkin, Hausawan Alimosho kuma Shugaban Majalisar Sarakunan Hausawa na wannan yanki. An haife ni a garin Idiyarba a nan Legas, ɗaya daga cikin matattarar ’yan Arewa a Legas, a ranar 5 ga watan Satumba, 1977. A garin Agege na taso, wanda shi ne gari mafi yawan al’ummar Arewa a Kurmi kuma na samu kaina a nan karamar Hukumar Alimosho, wato ƙaramar hukuma mafi girma da tarin al’umma tare da faɗin ƙasa a Legas. A nan ne Allah Ya ƙaddara na sami sarauta kuma cikin ikonSa sarakunan Hausawan yankin da na tarar suka ba ni goyon baya na zama jagoransu, saboda ganin irin tsarin da na kawo na neman haɗin kai a tasakanin ɗaukacin sarakunan da kuma mabiyan su.

Ko ya aka yi ka gai ga samun wannan sarauata?

Tun lokacin da na yi gida na tare a Unguwar Baruwa sai na lura da yadda ’yan Arewa mazauna yankin kan samu kansu cikin hali na tsaka mai wuya, kasancewar ba su da wani jagora a yankin, idan sun samu kansu a wani hali babu mai yin tsayin daka ya share masu hawaye. Hakan ne ya sanya na fara tunanin yadda zan ba da gudunmowata a wannan fuska, za ka ga jama’armu da kan zo daga Arewa, suna ƙananan sana’o’i kamar masu tuƙa babur da dai makamantansu, idan wani ɗan abu ya haɗa su da jami’an tsaro ko makamantan haka sai ka ga sun shiga wani hali saboda rashin wanda zai tsaya masu. Babbar matsalar da akan samu mafi akasarinsu ba su jin Turanci ko Yarabanci, ganin haka ne ya sanya ni kowane lokaci na yi kiciɓis da irin hakan sai in tsaya in tabbatar na shiga an warware matsalar. Sau dayawa in na fito za ni harkokin kasuwancina, nakan yi kiciɓis da irin wannan sai na bar harkokin gabana, na tsaya har sai na ga na karɓar wa mutanenmu hakƙoƙinsu, na yin rayuwa kamar kowane ɗan ƙasa. Ganin irin hoɓɓasar da nake yi ne al’ummar yankin suka nuna sha’awarsu cewa in zamo sarkinsu. Bayan da shirye-shirye suka kankama, muka nufi wajen babban basaraken Yarabawan karamar Hukumar Alimosho, wanda haƙƙinsa ne ya naɗa Sarkin Hausawa. To ashe tun a baya, akwai wanda aka so a bai wa sarautar Sarkin Hausawan, tun kafin zuwana yankin amma sai ya ƙi ba da himma ko da ya ga na zo za a yi mani sarautar sai ya nuna sha’awarsa. Ganin haka sai na janye na ce a ba shi, to ganin yadda cikin sauki na nemi masalaha na janye masa ne sai jama’a suka ce lallai ni na fi dacewa in jagorance su. To, a haka Allah Ya nufa na zama sarki, bayan da babban basaraken lardin ya amince sai fadar Sarkin Hausawan Agege ta yi mani naɗi, zan kuma cika shekara ɗaya a karagar mulki a watan Janairun shekarar 2018.

Ya aka yi har sarakunan da ka iske suka ba ka jan ragamar su?

Bayan da aka naɗa ni Sarkin Hausawan Baruwa, na nemi haɗin kan ɗaukacin sarakunan Hausawa da ke karamar Hukumar Alimosho, muka kafa majalisa sannan muka fito da tsarin tuntuɓar juna da yin taro a kai-a kai, ganin kyawawan sabbin tsare-tsaren da na bijiro da su ne ɗaukacin sarakunan suka yi yarjejeniya sannan suka amince da in zamo jagoransu, wato shugaban majalisarsu. To, a haka muke gudanar da ayyukanmu cikin yarda da juna tare da neman shawarwarin juna kuma hakan bai tsaya ga mu Hausawa kaɗai ba, domin tare muke aiki da sarakunan Yarabawa da na ƙabilar Igbo, muna da kyakkyawar alaƙa, muna kuma aikin tare domin ci gaban yankinmu da ma al’ummarmu baki ɗaya. A kodayaushe burinmu shi ne samun dauwamamman zaman lafiya domin sai da shi ne ake iya yin komai.

A baya, majalisarku ta shirya taro wanda ya sami kyakkyawan yabo daga Gwamnatin Legas, ko ya aka kai ga haka?

Eh, alal haƙiƙa a lokacin bikin Sallah Babba da ta gabata ne Majalisar Sarakunan Alimosho muka ga ya dace mu kira taron shuwagabannin gargajiya na al’ummar yankin, na ɗaukacin ƙabilun yankin tare da jami’an tsaro waɗanda suka yi mana bita da shuwagabannin al’ummah na ɓangaren gwamnati. Gannin yadda taron ya gudana tare da armashin da ya yi ne muka samu kyakkyawan yabo. A haka ne na samu lambar girmamawa daga hukumomi daban-daban na Jihar Legas, ciki har da lambar yabo da na samu daga kafar sadarwar ta ƙasa, inda suka karrama ni da lambar yabo ta sarki mafi ƙoƙarin sada zumunci. A lokacin ne suka karamma mai martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Alhaji Ramalan Yero da dai sauran manyan mutane daga sassa daban-daban na ƙasar nan sai kuma lambar yabo da babban birnin Legas ya ba ni, wato birnin Ikeja. A wannan lokacin an karrama ni tare da babban basaraken Yarabawa na Agege da Shugaban Majalisar Jihar Legas, Obasa. Wannan karramawa da aka yi mani ta ƙara mani ƙaimi a ƙoƙarin da nake don sama wa al’ummarmu mafita.