Kungiyar Hezbollah da ke Lebanon a ranar Juma’a ta harba wasu rokoki cikin kasar Isra’ila, a daidai lokacin da al’amura suka sake dagulewa tsakanin kungiyar da ke samun goyon bayan Iran da kuma kasar Yahudawan.
Ko a farkon makon nan dai sai da kasar Isra’ila ta kaddamar da hare-hare ta sama a kasar ta Lebanon a karon farko cikin shekaru bakwai, inda ita kuma a karon farko tun 2019, kungiyar ta Hezbollah ta dauki alhakin harba rokokin.
- Najeriya ba irin su Atiku ko Tinubu take bukata ba a 2023 – IBB
- Sojoji sun kashe ’yan bindiga 78 a dazukan Zamfara
Bayan harin dai, kasar ta Isra’ila ta ce ba ta fatan lamarin ya kazance zuwa mummunan yaki, a daidai lokacin da ru dunar kiyaye zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya a yankin ta yi gargadin cewa akwai babbar barazana a yankin, tana mai kira ga bangarorin biyu da su tsagaita wuta.
Ministan Tsaron Isra’ila, Benny Gantz ya yi kira ga kasar Amurka da ta umarci Gwamnatin kasar Lebanon ta tsawatarwa kungiyar ta Hezbollah daga ci gaba da harba rokokin zuwa kasarta.
Sai dai Hezbollah ta ce ta harba rokokin ne a wani fili da ke kusa da wata gona ta Shebaa da ke kan iyakar kasar ta Isra’ila.
Ta ce harin na mayar da martani ne ga hare-haren da kasar ta kai Kudancin Lebanon ranar Alhamis, irinsu na farko tun shekarar 2014.
Isra’ila dai ta ce Hezbollahta harba rokoki guda 19 ne, inda shida daga cikinsu suka fada kasar, yayin da ragowar kuma sojojinta suka kakkabo su kafin su kai ga dira kasa.
AFP