Hedkwatar Tsaro ta Najeriya ta zargi kamfanin dillancin labarai na Birtaniya, Reuters, da kokarin bata sunan Rundunar Sojin Najeriya ta salon aikin jaridarsu.
Daraktan yada labarai na hedkwatar, Manjo Janar Jimmy Akpor ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, a cewar Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN).
Akpor ya ce, Reuters ta ayyana shirya wasu jerin rahotani kan abin ya kira yakin da rundunar sojin take yi da ’yan ta’addar da ke yaki da sunan Musulunci a yankin Arewa maso Gabas na kasar, tsawon shekaru 13.
Sanarwar ta ce, shirin kamfanin dillancin labaran zai mayar da hankali kan abin da ya kira aikin zubar da ciki na dole ga matan da ’yan ta’addan suka yi wa ciki da kuma wani shiri na kisan yara kanana da ta ce sojojin ke yi a wani mataki na dakile ta’addanci.
Daraktan ya karyata wannan zarge-zargen da kuma kage, yana mai cewa, wannan abin kafar yada labaran ke shirin yi tsagwaron mugunta ce da bata suna ta hanyar amfani da aikin jarida.
“An hori jami’an rundunar sojin Najeriya da su ceci rai, su kuma kare dukiya, ko da za su rasa rayukansu a yayin hakan, musamman rayukan yara da mata da kuma tsaffi, kamar yadda yake a cikin dokokin aikin soji,” inji Manjo Janar Akpor.
Sannnan ya ce, Rundunar Sojin tana taimakawa da abinci da magunguna da kuma taimakon jinkai ga wadanda ’yan ta’addan suka tarwatsa tare hadin gwiwar Gwamnatin Jihar Borno.
Sai dai ya ce idanun kamfanin na Reuters hankalinsu bai kai nan ba, sai wani abin da babu shi babu kamar sa.