Hedikwatar Rundunar Tsaron Najeriya (DHQ) ta ce dakarunta sun yi nasarar kashe ’yan ta’adda 52 da kama 53 a wasu samame da suka kai jihohin Borno da Yobe.
Mai magana da yawun DHQ, Manjo-Janar Edward Buba, ne ya bayyana hakan yana mai cewa an kuma samu ’yan ta’adda bakwai da suka haɗa maza biyar da mata biyu da suka miƙa kansu ga sojojin.
- Diphtheria: Cutar mashaƙo ta yi ajalin mutum 10 a Jigawa
- Ban gamsu da hukuncin kotu kan zaben Bauchi ba, zan ɗaukaka ƙara – Sadique
Janar Buba ya ce an kuɓutar da mutum 61 da aka yi garkuwa da su a wurare daban-daban da ke ƙasar.
Ya kuma ce dakarun Operation Haɗin Kai a yankin Arewa maso Gabas, sun yi artabu da ’yan ta’addan a lokacin da suka kai samame, inda suka samu nasarar ƙwato makamai da dama.
A ɗayan ɓangare, ya ce dakarun Operation Delta Safe sun samu nasarar kama masu satar ɗanyen man fetur, inda suka kwace lita 496, 250 ta ɗanyen mai, injunan tuka-tuka guda huɗu, jiragen ruwa biyar da tankunan ajiye mai 57 da sauransu.
Janar Edward ya ce baya ga wannan, sojojin sun kwato harsasai daban-daban daga wajen masu aikata ta’asar.