Majalisar Wakilai ta ba wa Shugaban Rundunar Sojin Ruwa ta Najeriya Vice Admiral Ibok Ete Ibas sati daya ya je ya yi mata bayanin kudin haya Naira miliyan 11.5 da ya karba daga Ofishin Akanta Janar na Tarayya.
Kwamitin Majalisar kan Rundunar Sojin Ruwa ya kuma tisa keyar sojojin da suka wakilci Ibas a zamansa bisa jagorancin Darektan Kasafin Kudi na Rundunar, Kwamanda Murtala Ahmed, da cewa ba su wadatar ba.
“Idan Shugaban Rundunar Sojin Ruwan ba zai zo da kansa ba, to ya turo wani babban hafsa sosai zuwa gaban kwamitin, mun ba shi kwana bakwai kacal”, inji Shugaban Kwamitin Wole Oke, bayan Kwamanda Murtala ya shaida musu cewa Ibas ba zai samu halartar zaman ba saboda yanayin aiki.
Kwamitin ya kuma tura wakilai zuwa Jihar Osun domin bincikar ko an biya diyyar miliyan N30 ga al’ummomin da aka rusa wa gidaje domin gina hanyar ruwa ta Ugbaga a garin Osogbo da kuma Okoko a Jihar Ribas.
’Yan majalisar da za su yi aikin su ne Bimbo Ajide Sororo da Kolawole Oyetola da Zakari Mba da kuma Chinnedu Oga.