An tayar da jijiyoyin wuya a zauren Majalisar Wakilai yayin da aka kaure da hayaniya bayan wasu ’yan majalisar sun ki amincewa da rage kason da ake bai wa yankunan da ake hakar danyen mai a kasar.
A kan haka ne Majalisar ta jingine yin nazari kan kudirin dokar na man fetur biyo bayan zazzafar muhawarar da ’yan majalisar suka rika tafkawa.
Tun da farko dai Majalisar Wakilan ta amince da bai wa yankunan kaso 5 cikin 100 kamar yadda dokar man fetur ta PIB ta tanada, amma Majalisar Dattawa ta rage shi zuwa kaso 3 cikin 100.
Aminiya ta ruwaito cewa, Honarabul Chinyere Igwe na jam’iyyar PDP ne ya fara tayar da jijiyar wuya ta nuna kin amincewa da rage kason da ake bai wa yankunan.
Wakilinmu ya shaida yadda Honarabul Igwe ya rika daga muryarsa a zauren Majalisar duk don ya nuna kin amincewa da rage kason daga biyar zuwa uku cikin dari da ake ba yankunan.
Wannan hayaniya ta ci gaba da gudana har zuwa lokacin shigowar Kakakin Majalisar, Femi Gbajabiamila.
Ganin zuwan Gbajabiamila bai sa kurar hayaniyar ta lafa ba, saboda haka ya bukaci shugabannin Majalisar su yi ganawar sirri a kan batun.