✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Hayakin icen girki na kashe mutum 90,000 a Najeriya

Yawancin mamatan mata ne da kananan yara.

’Yan Najeriya akalla dubu casa’in ne ke rasuwa a sakamakon shakar hayakin icen girki a duk shekara, a cewar Gwamnatin Tarayya.

Ministar Muhalli, Sharon IKeazor, ta ce yawancin mutanen da shakar  hayakin icen girki ke yin jalinsu a kasar mata ne da kananan yara.

Da take jawabi ga taron tsarin yin girki ba tare da hayaki ba na 2021, ministar ta ce, “Amfani da makamashin biomass (shuke-shuke) a wajen girki da dumama abubuwa yana kara kawo matsi ga muhalli da albarkatun kasa.

“Sannan yana barazana ga rayuwa da lafiyar masu amfani da shi, wadanda da yawancinsu mata ne da kuma ’ya’yansu kananan da ke biye da su.”

Ta ce a tsawon shekaru, ma’aikatarta tana goyon bayan a aiwatar da tsare-tsaren da za su tabbatar da yin girki ba tare da hayaki ba a Najeriya domin rage illa ga shuke-shuke da kuma kare muhalli.