✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hawan Daushe: Yadda Sarkin Zazzau ya karɓi gaisuwar sallah

Sarkin ya karɓi gaisuwar sallah ne a ranar hawan Daushe a Zariya.

Mai Martaba Sarkin Zazzau, Ahmad Nuhu Bamalli, ya karɓi gaisuwar sallah daga baƙi daga ciki da wajen ƙasar nan a lokacin bikin hawan Daushe a Zariya.

Sarkin ya karɓi gaisuwar sallah a fadarsa da ke Zariya, inda ya yi wa ɗaukacin al’ummar Musulmi fatan alheri da kuma fatan Allah Ya karɓi ibadansu.

Kazalika, Sarkin ya yi kira ga shugabanni da su tashi tsaye wajen magance matsalar ’yan fashin daji da ke yin garkuwa da mutane.

Ga hotunan yadda Sarkin ya karɓi gaisuwar sallah daga baƙi: