✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hauhawar farashi ya ragu zuwa kashi 32.15 — NBS

Sai dai hukumar ta ce farashin ya ƙaru idan aka kwatanta da watan Agustan 2023.

Duk da hauhawar farashin kayayyaki da ake fama da shi a faɗin Najeriya, Hukumar Kididdiga ta Ƙasa (NBS), ta sanar da cewa hauhawar ta ragu zuwa kashi 32.15 a watan Agusta da kuma kashi 33.40 a watan Yuli, 2024.

Wannan yana nuna cewa hauhawar farashi ta ragu da kashi 1.25 a watan Agusta, duk da tsadar abincin da ake fama da ita.

Sai dai idan aka kwatanta da watan Agusta 2023, hauhawar farashi ta ƙaru da kashi 6.35, domin a wancan lokacin farashin yana kashi 25.80.

NBS ta bayyana cewa, “Wannan yana nuna cewa hauhawar farashi ta ƙaru a watan Agusta 2024, idan aka kwatanta da watan Agusta 2023.”

Hauhawar farashi a watan Agustan 2024 ta kasance kashi 2.22, inda ya ragu da kashi 2.28 a watan Yuli 2024.

A taƙaice, wannan ya nuna an samu ƙarin farashin kayayyaki kaɗan a watan Agustan 2024, idan aka kwatanta da watan Yuli 2024.

Ko da yake tsadar rayuwa na ci gaba da tasiri, sakamakon ƙarin farashin man fetur da aka samu sama da kashi 354.