Farfajiyar gidan Baturen Hawan-sa
Harabar hasafin hau-hawar harasa
Kalaman kai-kawon karsashin kilisa
Kinkimar kaurara kurin kumsa
Fahimtar fannoni masana sun farfasa
In an ci gurasa
A hada da masa
Ga wasa-wasa
A kwanon tasa
A ji dadi a warwasa
Na-kwaciri tuni ya kosa
Ya gayyaci masu fursa
Su zo sui susa
Kar su bari a gurgusa
Nuku-nukun magabta a fallasa
An yi watsi da sa-in-sa
Ko matsin lambar da aka tursasa
Gwanlangwaso da kwalisa
Kantakaryar kwarkwasa
A dai dage a ci gasa
Kwalliya ce ai a dandasa
Gidan bikin ma fa a karasa
Baje-koli a karkasa
Ayyuka wasa-wasa
Garkamamun kofofi a kwankwasa
An dai yi biki
Wasu har da wage baki
Harshen uwar uba ake aiki
Dalibai na ta cin maki
Al’umma cike da mamaki
An dai baje kasidu
Dibge da watsattsaken takardu
Kan al’adu
Masana dai sun sadu
Kamar yadda aka baje a jaridu
Ladarshafi
Tai wa Hawan-sa hasafi
Ta baje batutuwa a shafi
Tare a digon aya da wakafi
Lallai mui musu tafi
Amiyawan aminai
Bar batun tara taro da nai
Baje na-mujiyar ganai
Don tsakuro bayanai
Kan kasuwacin kunduge aninai
Babban bakin Ce-ce-ku-ce
Nan ma an saki zance
Babu ka-ce-na-ce
Balantana zaurance
Iyaka dai kintace kwatance
Ai komai a zamanance
Kar a sakankance
Har sai an tanance
An san nagartacce
Illoli a bambance
Ka da a dimauce
A zo ai ta waskace-waskace
Da yawan kauce-kauce
Wai ana gudun karce-karce
A dai yi ta karance-karance
Muna ta kade-kade
Raye-raye da gyade-gyade
Ciye-ciye da tande-tande
Kalmomi an bi an markade
Yaushe za a debo zumar dade
Wasannin gargajiya
Gadar adon-gari
’Yan lalle na ta zabari
Kowa dai yai kokari
Hau-hawar hawan-sa ta zagaya
Nadin dambe
Bagun bebe
Kawanyar zobe
Kariyar takobin kwabe
Yau da gobe
Wa ya kirkiro ranakun duniya
Sai ai ta nunin danniya
Kunzugun annakiya
Kumbiya-kumbiya da kamuya-muya
Nagargarun ayyukan nuniya
Lamurjen lakarka ta sara
Kunun zakin tsululun gasara
Zubin zabibin kulora
A saisaita a gyara
Kar su dankare a mara
Wasu sun iya alamara
Shaci-fadin al’amura
Don kawai a tayar da kura
Lallai mu tashi mu zabura
Nagargarun ayyuka ai ta kira
Shu’umcin sharrin sharholiya
Shashancin shagalin shan miya
Shantakewar shan shayin modiya
Sha’anin sha’awar shalliya
Shirmen mamakon murdiya
Rankwafawar rugurguza rubutu
Kambama kambin kassara karatu
Surutun susucewar satu
Karime-karimen kutu-kutu
Kalaman kalmashe kantu
Ku daina carar carki
Da ce-ce-ku-cen cin tsaki
Kar a karke da bugun taiki
An manta da jaki
Kun ga an dau alhaki
Hau-hawar harabar hawan-sa
Hantsilawar hajijiyar hobbasa
Ranar rugumniyar rassa
Mamungar maganganun marisa
Fagamniyar fangimar farin-sa
Ingarman Ingausar Ingilishi
Inda-indar indararon Ibilishi
Binibinin bin bashi
Bushe-bushen bazuwar bushi
Katantanwar kai-kawon karsashi
Logar luggar li’irabin Larabcin Larabawa
Aji-ajin Ajamin Ajamawa
Tubalin tarairayar Turancin Turawa
Sunkurun sungumar Sinawa
Indiyancin Indira Gandin Indiyawa
Haruffan Haurobiyawa
Hade-haden harhadawa
Harkokin Hindiyawa
Hada-hadar Habashawa
Himmar hikimomin haskakawa
Yayime-yayimen ’yan yawa
Yaushin yankwanewar yunwa
Yari-yarin yarfen yarawa
Yake-yake yagalgalawa
Yamutsin yunkurin yakicewa
Kalmashe-kalmashen kanbama kalamai
Bambamin buga bama-bamai
Juriyar jajircewar jarumai
Masanan managartan malamai
Guiwar gande-ganden gwarmai
Nauyayyar nunin nakasa
Hautsinin hau-hawar harsuna
Bambance-bambancen batutuwan bakuna
Babu bakacen burtuntuna
Sunce sasarin sansanin sa-in-sa
Harkallar haramben handama
Hakilon harigidon hadama
Hatsaniyar hargowar harama
Hargagin haddasa husuma
Hasashen hukuncin hukuma
Ranar raunin raunana
Rigabzar ragargazar raguna
Rangajin rungumar rigima
Ririta rummacen rama
Raba ribar rabon rumfuna
Harafi-harafi
Kalmomi masu karfi
Jimloli jefi-jefi
Sadarar sirrin tasarufi
Cikar aya ai wakafi
Duhun dundum durundum
Dundumin dumu-dumu dum
Dumuiniyar damu dungurungum
Dawurwurin daga dururum
Dallakin dolancin dulum
Dungun dillalai
Damin dubun dubbai
Dagar Dabai da Dubai
Dabarbarun dandamalin dakalai
Dillanci dole da dalilai
Kiriniyar rashin ji
’Yan dugwi-dugwi sui ta gunji
Ina mata da miji
Ku nemi maganin kurji
Da ingancin uwar jikin magaji
Manhjar maje-haji
A iya sarrafa kajiji
A ci naman kaji
A ji karfin tada kwanji
Tare da taimakon Ubangiji
Ba ni fura-mai-kyau
N sha a yau
Gobe in yi kyau-kyau
Darandakau
Ga walwala sakayau
Sakanni-in-dire
Ilimu ke hana a dare
Hanya duk an share
Kimar matsayi a dare
Al’umma ta murmure
A kauce wa sare-sare
Kwalisar kwanare
Kai-kawon ’yan ta-more
Su samu wuri su share
Sui ta al’umma bare-bare
Jam’in jama’ar jami’o’i
A karade kowane zira’i
Don kauce wa balbalin bala’i
tun daga safe zuwa isha’i
ai ta samun sa’a kowane sa’i
kinkimi kimiyya
fasahar kere-kere
fanoni a tattare
watsattake a yi shi a tare
sai mu kai ga gacin ganiya
Sagaraftun sarrafa sinadarai
Ilmin sanin tsirrai
A halittu a duba birai
Cikinsu akwai jarirai
Da manyan ja’irai
Daga likafar likitanci
Bokan Turai
A tarairayi rai
Binciken ayyukan kwarai
Aiki na daban da kanikanci
Batun bisashe
A daina duk wani hasashe
Ko dabarbarun kwashe-kwashe
Tuni gari ya washe
Mu killace su a kowane sashe
Gayaunar garka
Gararumar rani da kaka
Hantsin hantsewar hatsi a haskaka
Kayan marmari ai musu tufka
Hakan take jika da kaka
An daukeku kanwar lasa
Gajeriyar kuka kasa-kasa
Jarfar jibar jibga tusa
Kun sha kisisina da kissa
Haka akai ta kafa muku kusa
Larurar lulawar lulaye
Logar lauye-lauye
Laulayin alaye
’Ya’ya da iyaye
Kun bar ko’ina an mamaye
Mui wa kawunanmu tanadi
Mui kasaken jin magabata da gargadi
Kar mu bari sai badi
Mai-duka yai mana budi
Sai mu samu lumanar sanadi