✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hatsarin tankar mai ya hallaka mutum 2 a Neja

Shaguna da babura da motoci da dama ne kuma suka Kone a hatsarin.

Akalla mutum biyu ne suka rasu a hatsarin tankar mai  a garin Enagi, hedkwatar Karamar Hukumar Edati ta Jihar Neja.

Wani ganau ya shaida wa wakilinmu cewa lamarin ya faru wajen misalin karfe 11:00 na safiyar ranar Lahadi.

A cewar Malam Hassan, wani wanda shi ma ya rasa shagonsa na gefen hanya a hatsarin ya ce tankar man ta yi taho-mu-gama ne da wata babbar motar kamfanin Dangote.

A cewarsa, “Tankar man na tahowa ne daga hanyar Mokwa, yayin da ita kuma motar Dangoten wacce ke zuwa daga Bida ta yi yunkurin wuce tankar, aka sami matsala suka yi karo, tankar ta kama da wuta.

“Shaguna da baburan da aka ajiye a gefen hanya da gine-gine da dama ne suka kone,” inji Malam Hassan.

Shi ma wani mazaunin inda abin ya faru, Muhammad Kitabu Enagi ya ce, “Zuwa yanzu, mutum biyu ne aka tsinci gawarwakinsu, amma motoci da yawa sun kone.

“Sai an dauke su ne za mu iya tabbatar ko akwai wasu karin mutanen da suka mutu,” inji shi.

Kwamandan Shiyya na Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC) a Jihar Neja, Musa A. Mohammed ya tabbatar wa wakilinmu faruwar hatsarin.

Ya ce, “Hatsarin ya ritsa da wata tankar mai ne da wata tirela mallakar kamfanin Dangote da suka yo taho-mu-ga, kuma ya zuwa yanzu, mutum biyu ne suka mutu.”