✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hatsarin mota ya yi ajalin mutum 30 a Chadi

Hatsarin ya yi ajalin sama da mutum 30, yayin da mutum 50 suka ji rauni.

Akalla fasinjoji sama da 30 ne suka mutu a tsakiyar kasar Chadi, yayin da wasu 50 suka samu raunuka daban-daban lokacin da wasu motoci guda biyu suka yi taho mu gama.

Rahotanni sun bayyana cewar hatsarin ya faru a ranar Lahadi da daddare lokacin da motocin safa ke tafiya a kan hanyar zuwa birnin Abeche da ke Chadin.

Sakataren Yankin Batha ta Yamma, Abdelaziz Hisseine yac e adadin mutanen da suka mutu ya kai 33, yayin da wadanda suka jikkata suka kai 54, kuma tuni aka kwashe masu raunuka zuwa asibitin Abeche.

Ma’aikatar sufurin Chadi ta ce an kaddamar da bincike a kan hatsarin wanda ake yawan samu saboda rashin hanyoyi masu inganci da kuma motocin da bai dace a tuka su a kan hanyoyi ba.

Shugaban kasa Mahamat Idris Deby ya aike da sakon ta’aziya ga iyalan wadanda suka mutu a shafinsa na Facebook, yayin da ya gargadi masu ababen hawa da su guji tukin ganganci.