Ana fargabar mutum 17 sun mutu a wani mummunan hatsarin mota da ya auku da Yammacin Talata a yankin Irepene da ke babbar hanyar Abuja zuwa Lokoja a jihar Kogi.
Aminiya ta samu cewa hatsarin ya auku ne a tsakanin wata Mota kirar Toyota Hiase da kuma wata babbar motar matafiya dauke da fasinjoji bila adadin yayin da suke kan hanyarsu kishiyoyin juna.
- ’Yan bindiga sun sace mutum 16 a kauyen jihar Katsina
- Kotun Musulunci ta sa a kamo mawaki Rarara kan ‘boye matar aure’
Rahotanni sun tabbatar da cewa mutum 15 sun mutu ne nan take, yayin da ragowar biyu da suka samu munanan raunuka suka ce ga garinku nan bayan an garzaya da su asibiti.
Kwamandan Hukumar Kiyaye Hadurra na jihar Kogi, Solomon Agure ya tabbatar da aukuwar lamarin da cewa motar Toyota tana kan hanyar zuwa garin Auchi na jihar Edo a yayin da babbar motar matafiyan ta sharo daga Okene.
Mista Agure ya shawarci direbobi da su rika takaita gudu da motoci musamman idan duhu ya kawo jiki tare da kiyaye dukkan ka’idodin tuki.
Ya ce “yana da matukar muhimmanci ga direbobi su rika iyakance gudunsu kamar yadda doka ta tanada ga motocin haya da kuma na masu zaman kansu,” inji shi.
Agure ya ce hukumarsu ta tanadi akalla jami’ai 522 domin tabbatar da ba a samu cunkoson ababen hawa ba a wannan lokaci na shagulgulan bikin Kirsimeti da na sabuwar shekara da ya kawo jiki.