Wani matashi dan asalin Jihar Kano, mai yi wa kasa hidima a Jihar Adamawa ya hadu da ajalinsa a wani hatsarin mota da ya rutsa da shi.
Hussaini Sa’idu Abdullahi mai shekara 25 a duniya, wanda ya karanci fannin kasuwanci a wata Jami’a da ke Kasar Sudan, ya gamu da ajalinsa ne a ranar Talata.
- Dubun matar da ake zargi da satar yara ta cika a Jihar Nasarawa
- Buhari ya tafi Dubai tare da rakiyar Ministoci 10
Majiya daga iyalan matashin, ta shaida wa Aminiya cewar hukumar NYSC ta sauya wa matashin Jihar da zai yi hidimar kasa daga Adamawan zuwa Nasarawa, kuma kan hanyarsa ta tafiya can ne ya gamu da ajalin nasa.
Majiyar ta kuma ce an binne matashin a unguwar ‘Ring Road’ da ke Jihar Kano, kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.
“Hussaini matashi ne mai hankali. Yana da azama da jajircewa a rayuwa. Allah ya fi son shi fiye da yadda muke son shi. Don haka ba mu da abin da za mu yi face mu dauki dangana. Muna fatan Allah ya masa rahama,” cewar majiyar.
Mahaifin matashin, Saidu Abdullahi ya ce ya yi rashi babba, na mutumin da ya raina cikin aminci kafin rasuwarsa.
“Ina godiya ga duk wanda ya samu damar halartar jana’izarsa tare da jajanta mana, Allah ya ba wa kowa lada. Iyaye masu raino ne, amma Allah madaukakin Sarki shi ne mai iko kan abin da ya hallita tare da daukar kayansa a lokacin da ya so.
“Ina yi wa ubangiji godiya da ya ba ni ikon yi masa tarbiyya, tare da rainonsa ta hanyar da ya dace, har zuwa lokacin da ajalinsa ya riske shi,” kamar yadda mahaifin matashin ya bayyana.