✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hatsarin mota ya yi ajalin mata 2 a kan hanyar Kaltungo-Cham

Hukumar ta ce tuni aka garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa asibiti domin yi musu magani.

Hukumar Kiyaye Hadura ta Ƙasa (FRSC) a Jihar Gombe, ta tabbatar da mutuwar wasu mata biyu a wani hatsarin mota da ya rutsa da su a kan hanyar Kaltungo zuwa Cham.

Kwamandan hukumar a jihar, Samson Kaura, ya ce hatsarin ya rutsa da mutum bakwai; maza biyar da mata biyu.

Ya bayyana cewa mata biyun da ke cikin motar sun mutu nan take, kuma an kai gawarsu asibitin Kaltungo.

Kazalika, ya ce waɗanda suka samu raunuka an garzaya da su asibiti don yi musu magani.

Kaura, ya ce hatsarin ya faru ne saboda gudun wuce ƙima, wanda hakan ya sa ya gargaɗi direbobi da su dinga taka-tsantsan yayin da suke tuƙi.

“Dole ne direba ya tabbatar da cewa yana gudu kamar yadda doka ta tanadar, sannan ya guje wa zarce wani ba bisa ƙa’ida ba,” in ji Kaura.

Har wa yau, ya ja hankalin fasinjoji da su riƙa duba lafiyar mota da yanayin direba kafin su hau mota domin yin tafiye-tafiye.

“Fasinjoji su daina hanzarin hawa mota ba tare da tabbatar da lafiyarta da kuma halin direba ba, saboda wasu lokutan ana samun direba a cikin yanayin maye,” a cewarsa.