Wani mummunan hatsarin mota a Jihar Jigawa ya yi sanadiyyar rasuwar iyalai ’yan gida daya su hudu.
Lamarin ya faru ne ranar Asabar lokacin da suke hanyarsu ta zuwa garin Malam Madori domin halartar taron biki inda motarsu ta kife tare da hallaka mutum uku nan take.
- ‘Ina hada maza da mata su har su yi haure’
- Manyan motoci sun tare babbar hanyar Kaduna
- Yaron da ya fara kasa kaya a kwali ya yi shagon kansa a kwana 10.
Rahotanni sun tabbatar da cewa hatsarin ya faru ne a garin Danladin-Gumel, na Karamar Hukumar Gumel ta Jihar Jigawa.
Da yake tabbatar da lamarin, wani makusancin mamatan, Malam Shehu Yusuf Kazaure ya ce dukkannin mamatan ’ya’yan Hajiya Safiya Mohammed ne, wacce darakta ce a bangaren manyan makarantu a Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Jigawa.
A cewarsa, “Lamarin ya faru ne da yammacin ranar Asabar kusa da garin Danladin-Gumel na Jihar Jigawa. Kuma uku daga cikin ’ya’yan Hajiya Safiya; Fati, Abba da Zainab nan take su ka mutu.
“An karasa da gawarwakin zuwa Malam Madori inda a can kuma Hanan, wacce ’ya ce ga daya daga cikin mamatan (Zainab) ita ma ta riga mu gidan gaskiya.
“Akwai tashin hankali a cikin lamarin matuka saboda yawancinmu mun kasa rike hawayenmu domin alhini. Mutuwar mutum hudu ’yan gida daya akwai dimuwa sosai a ciki, Allah ya gafarta musu”, inji Shehu Kazaure.
Ya ce tuni a ka yi jana’izar mamatan da safiyar Lahadi a garin na Malam Madori kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.