✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hatsarin mota ya lakume rayuka 11 a Kano da Kwara

Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta tabbatar da rasuwar akalla mutum bakwai saboda hatsarin mota a dab da shatale-talen Mundubawa dake kan titin Hadeja…

Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta tabbatar da rasuwar akalla mutum bakwai saboda hatsarin mota a dab da shatale-talen Mundubawa dake kan titin Hadeja Road na karamar hukumar Nasarawa dake jihar.

Kakakin hukumar, Sa’idu Muhammad shine ya tabbatar da hakan ranar Laraba a wata sanarwa.

Ya ce hatsarin ya faru ne da misalin karfe 5:27 na safiyar ranar ta Laraba lokacin da wata babbar motar tirela ta yi taho-mu-gama da wata a-kori-kura.

Kakakin ya ce ba su yi wata-wata ba suka garzaya da su Asibitin Sir Sunusi dake Kano inda nan take likita ya tabbatar da rasuwar bakwai daga cikinsu.

Kazalika ya ce mutum biyu kuma da suka sami raunuka na can suna samun kulawa a asibitin.

A wani labarin kuma, akalla mutane hudu ne suka rasu a wani mummunan hatsarin motar a garin Offa na jihar Kwara.

Hatsarin dai ya faru ne da misalin karfe 10:27 na safiyar ranar ta Laraba tsakanin wata mota kirar Camry da wani babur mai kafa uku.

Rahotanni dai sun nuna cewa motar, wacce wani bakanike ke tukawa ta fadawa babur din ne inda ta kashe mutane ukun dake cikinsa da kuma wata mace da take kasuwanci a gefen hanya.

Wani wanda lamarin ya faru a kan idonsa ya ce akwai wasu daliban Kwalejin Fasaha ta Offa wadanda ke cikin babur din da su ma suka sami raunuka.

Ya kuma ce wasu fusatattun matasa sun bankawa motar wuta saboda sun ce tukin gangancin direbanta ne ya haddasa hatsarin.