✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Hatsarin mota ya ci mutum uku a Neja

Wasu mutum 33 na asibiti sakamakon hatsarin babbar motar

Mutum uku sun sheka barzahu wasu 33 kuma suka jikkata a wani mummunar hatsari da ya uku a kan gadar Gwachipe da ke yankin Lambatta a Jihar Neja.

Kwamandan Hukumar Kiyaye Hadurra ta FRSC reshen Suleja-Lambatta, Joel Dagwa ne ya tabbatar da faruwar lamarin yayin zantawarsa da manema labarai.

Ya bayyana cewa abin ya faru ne da wata tirela makare da kaya da ke gudun wuce ka’ida, inda ta ce ta kwace sannan ta kife a kan gadar.

Dagwa ya ce fasinja 36 ne a cikin motar da ta taso daga Kano zuwa Legas a lokacin da abin ya faru.

Jami’in ya kara da cewa nan take mutum uku suka mutu, wasu 33 kuma suka samu rauni a cikin motar wadda ko lamba ta da ita.

Sai dai ya ce tuni jami’an FRSC suka kai agajin gaggawa wajen da hatsarin da ya faru a Laraba.

Dagwa ya ce an garzaya da wadanda suka samu rauni zuwa cibiyar lafiya ta Gawu Babangida, mamatan kuma an kai su dakin ajiyar gawa da ke Sabon Wuse.