Mutum biyu sun ɓace a sakamakon hatsarin ƙwalekwale a Rafin Zindiwa da ke Ƙaramar Hukumar Gamawa a Jihar Bauchi.
Kwalekwale mai ɗauke da fasinjojin ya yi hatsarin ne a safiyar ranar Asabar.
Mai magana da yawun ’yan sanda a Jihar Bauchi, Mohammed Ahmed Wakil, ya bayyana cewa mutum shida ne a cikin kwalekwalen lokacin da ya yi hatsarin.
Wakil ya ce duk fasinjojin ’yan kauyen Zindiwa ne, direban kuma ɗan ƙauyen Wabo.
- Akwai yiwuwar ƙara farashin fetur a Najeriya
- Yadda ’yan banga suka yi wa Fulani 11 ’yan gida ɗaya kisan gilla
Jami’an ya ce ana ci gaba da aikin ceto domin gano ragowar mutanen da ba a gani ba.
Ya ce fasinjojin na amfani da kwalekwalen wajen sufuri ne bayan ambaliya ta shafe babbar hanyar da ta haɗe garin Gamawa da sauran ƙauyukan yankin.
Sakamakon haka al’ummar yankin suka koma amfani da kwalekwale domin zirga-zirga a yankin musamman a ranakun kasuwa.