✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hatsarin kwale-kwale ya kashe mutum 15 a Adamawa

An kuɓutar da mutum bakwai yayin da ake ci gaba da neman bakwai.

Aƙalla mutum 15 ne suka mutu bayan da wani kwale-kwale ya kife a jihar Adamawa kamar yadda BBC ya ruwaito.

Lamarin ya faru ne da maraicen ranar Juma’a lokacin da kwale-kwalen ɗauke da fasinjoji 23 ciki har da manoma da ’yan kasuwa da ƙananan yara, ya taso daga ƙauyen Rugange zuwa garin Yola a kogin Njuwa.

Rahotonni sun ambato wani jami’in ƙungiyar bayar da agaji ta Red Cross na cewa an tsamo gawarwaki hudu a wurin da lamarin ya faru, yayin da ake ci gaba da aikin ceto.

Ya ce iska mai ƙarfi ce ta tilasta wa ruwa shiga cikin kwale-kwalen, wanda nan take ya kife da fasinjojin da ke cikinsa.

Ya yi kira hukumomin jihar da su samar wa al’ummar ƙauyen Rugange, waɗanda ke fuskantar matsalar ambaliya duk shekara, jirgin ruwa mai amfani da inji.

Sakataren hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar ADSEMA, Muhammad Amin Sulaiman, ya ce an kuɓutar da mutum bakwai yayin ake ci gaba da neman bakwai.