✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hatsarin jirgin sama 11 da suka kashe hafsoshin sojin Najeriya

A shekara hudu hatsarin jiragen sojin Najeriya sun ci rayukan manyan sojoji akalla 33

Najeriya ta yi asarar manya-manyan dakarun soji akalla guda 33 a sanadin hatsarin jirgin sama 11 da aka samu daga 2015 zuwa 2022.

A ranar Talata ne wasu matukan jirgin sama na Super Mushark da ya yi hatsari a makarantar horas da tukin jiragen sama da ke Kaduna, Laftanar Alkali da Laftanar Karatu, suka rasa rayukansu bayan kammala karatunsu a Jami’ar Soji ta NDA.

Bayanai sun ce hafsoshin biyu na daga cikin sojojin saman Najeriya da suka dawo daga kasar Pakistan a watan Afrilun 2021, inda suka samu horon wata shida kan yadda ake kera jiragen yaki.

Rundunar Sojojin Sama ta Najeriya (NAF), ta samu jiragen Super Mussak guda 10 daga kasar Pakistan a tsakanin 2017 zuwa 2018 domin inganta horar da dakarunta.

Hatsarin jirgin na ranar Talata shi ne na hudu da jiragin NAF suka yi cikin ’yan watannin nan.

Wata 11 da suka gabata, Babban Hafsan Sojin Kasa, Manjo-Janar Ibrahim Attahiru, da wasu manyan jami’an soji 10 sun rasu a wani hatsarin jirgin sama da ya rutsa da su a Kaduna.

Daga 2015 zuwa 2021, Najeriya ta hatsarin jirgin soji 11 wadanda suka yi sanadin halaka jami’an soji akalla 33.

A ranar 21 ga Maris 2021, wani jirgin sama kirar Beechcraft King Air 350i, ya yi hatsari a Abuja tare da kashe duk sojoji bakwai da ke ciki.

Har wa yau, a watan Afrilu 2021, wani jirgin yaki kirar Alpha Jet ya fado yayin da ya ke tallafawa sojoji a Arewa maso gabashin Najeriya.