✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Hatsarin jirgin ruwa ya yi ajalin mutum 30 a Neja

Mutum bakwai ne har yanzu ba a gani ba yayin da tuni an ceto kimanin mutum 65.

Gwanayen ninkaya sun tsamo gawawwakin mutum 30 da suka mutu sakamakon kifewar wani jirgin ruwa ranar Asabar a Jihar Neja.

Mutum bakwai ne har yanzu ba a gani ba yayin da tuni an ceto kimanin mutum 65 tun bayan nutsewar jirgin ruwan a kan hanyar zuwa kauyen Tijana da ke Karamar Hukumar Munya ta jihar.

Jirgin wanda ya dauko dakon akalla mutum 100 ciki har da mata da kananan yara, ya kife ne a tsakiyar ruwa da misalin karfe 6.00 na yammacin Asabar.

Aminiya ta ruwaito cewa, jirgin na dauke ne da mutanen da ke hanyarsu ta dawowa daga cin kasuwa a kauyen Zumba na Karamar Hukumar Shiroro ta Jihar.

Sarkin Kasuwar Zumba, Adamu Ahmed, ya tabbatar da faruwar lamarin, wanda a cewarsa ana ci gaba da aikin ceto bayan gano gawawwakin mutum 30 da suka riga mu gidan gaskiya.

A nasa bangaren, Shugaban Hukumar ba da agajin gaggawa ta Jihar Neja, Ahmed Inga, ya ce hatsarin ya auku ne yayin da jirgin dauke da akalla mutum dari ya daki wani kututture da ke cikin ruwan.

“Sanadiyar haka ne jirgin ya kife kuma kawo yanzu an gano mutum 65 a raye, sai guda bakwai da ake ci gaba da nema da kuma karin wasu 28 da suka riga mu gidan gaskiya,” in ji shi.