✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hatsarin jirgin Kebbi: An kara gano gawa 13

Ana ci gaba da aikin ceto bayan kifewar jirgin mai dauke da mutum kusan 200.

An gano karin gawarwaki 13 daga cikin fasinjojin jirgin ruwan da ya kife a Jihar Kebbi.

Tun a ranar Laraba aka gano gawarwaki biyar bayan hatsarin jirgin da ke dauke da kusan mutum 200 daga Jihar Kebbi zuwa Neja.

Jirgin ruwan ya kife ne a yankin Tsohuwan Labata da ke Karamar Hukumar Ngaski ta Jihar Kebbi, bayan sa’o’i da fara tafiyar.

Wani mazaunin kauyen Warra, Adamu Umar Warra, ya shaida wa wakilinmu ta waya cewa ana sa ran masu aikin ceto za su gano karin gawarwaki.

“Jirgin ruwan ya dauki fasinjoji 180 da babura 30 kirar Bajaj. Fasinojin na hanyarsu ce ta zuwa kasuwa a Malele da ke Karamar Hukumar Borgu ta Jihar Neja daga Kebbi, kuma hatsarin ya faru ne awanni kadan bayan tashinsu,” inji Manajan Hukumar Kula da Rafuka ta Najeriya (NIWA) a Yauri, Jihar Kebbi, Yusuf Birma.