✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hatsarin jirgin kasa ya kashe kusan mutum 300 a Indiya

An yi ammana hadarin shi ne mafi muni tun daga shekarun 1990.

Akalla mutane 288 ne suka mutu yayin da fiye da 850 suka jikkata a wani mummunan hatsarin jirgin kasa da ya afku a kasar Indiya.

Alkalumma na hasashen shi ne hatsarin jirgin kasa mafi muni da kasar ta gani cikin sama da shekaru 20.

Har ya zuwa wayewar garin Asabar masu aikin ceto da kokarin gano masu sauran nunfashi karkashin karagun jiragen kasa guda ukun da suka kife sakamakon hatsarin na Yammacin Juma’a.

Hotunan wurin da hatsarin ya afku sun nuna tarkacen karagun jiragen da kuma yadda jinni ke malala a yankin Balasore, na Jihar Odisha da ke Gabashin India.

Hadduran jiragen kasa dai ba sabon abu bane a kasar Indiya, mafi muni da kasar ta gani shine a shekarar 1981, lokacin da wani jirgin kasa ya kauce hanya tsallaka wata gada a Bihar ya fada cikin kogin, inda nan take mutane tsakanin 800 zuwa 1,000 suka mutu.

To sai dai an yi ammana da cewa hadarin na ranar Juma’a shi ne mafi muni tun daga shekarun 1990.

Babban Sakatare na Jihar Odisha Pradeep Jena ya tabbatar da cewa, kimanin mutane 850 ne suka jikkata kuma sun kwance a asibitoci sakamakon hadarin.