A farkon bana ce Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya (NiMET) ta fitar da sanarwar cewa ana hasashen bana ma za a yi ruwan sama sosai, inda ta yi gargadin cewa akwai yiwuwar fuskantar ambaliya mai girma.
Idan ba a manta ba, a bara an fuskanci ambaliyar ruwa mai tsanani, wadda ta jawo asarar rayuka da miliyoyin Naira.
Aminiya ta lura a duk shekara akan yi gargadin yiwuwar fuskantar ambaliya, amma ba a cika daukar matakan kariya daga gare ta ba, inda a lokuta da dama, wuraren da ake fuskantar ambaliyar duk shekara suke sake fuskantar lamarin ba tare da daukar mataki ba.
Aminiya ta kuma gano duk shekara Gwamnatin Tarayya tana ware biliyoyin Naira don kula da muhalli, sai dai kuma akan rasa inda kudaden suke zurarewa.
A Jihar Taraba, fiye da garuruwa 100 ne suke bakin manyan kogunan jihar wadanda suka fuskanci matsalar ambaliya a bara.
Wadannan garuruwan suna cikin kananan hukumomi takwas daga cikin 16 da ke jihar. Kananan hukumomin sun hada da Lau da Karim Lamido da Gassol da Ibbi. Sai ArdoKola da Wukari da Donga da Bali .
Dubban al’ummar wadannan yankuna suna gudanar da ayyukan noma a gaban koguna da ake samun matsalar ambaliya a lokuta da dama.
Kogunan sun hada da Kogin Binuwai da na Taraba da Kogin Lamurde da kuma Kogin Donga.
A bara an samu mummunar ambaliya da ta haifar da asara mai yawa na kayan amfanin gona da dabbobi da gidaje.
Amma duk da barnar da ambaliyar ta haifar mazauna yankunan bakin kogi a Jihar Taraba sun koma gidajensu ba tare da tsoron sake fadawa cikin matsalar da ambaliyar ta haifar ba.
Binciken da wakilin Aminiya ya gudanar ya gano cewa wadanda ambaliyar ta lalata wa gidajensu sun gyara gidajen su sun koma.
Wuraren da suka fi fuskantar ambaliya a bara sun hada da garuruwan Zip da Jen da Gurowa da Lau da Kambari da Dampar da Ibbi da Tella da Donga da Mayo Reniyo da sauran garuruwa masu yawan gaske.
Shugabanin al’umma da ’yan siyasa sun fadakar da al’ummarsu hadarin da ke cikin rashin kauracewa inda aka samu matsalar ambaliyar. Sarkin Mutum-Biyu Alhaji Sani Muhammed ya shawarci al’ummar masarautarsa cewa hukuma ta yi gargadin cewa za a sake samun aukuwar ambaliyar a daminar bana.
Amma duk da gargadin da aka yi wa jama’a mazauna bakin manyan koguna a jihar sun yi kunnin uwar shegu sun ci gaba da zama.
Sai dai Aminiya ta lura cewa komawa yankunan da mutanen suka yi bai rasa nasaba da rashin daukar mataki daga gwamnati bayan gargadin da ta yi kawai.
A Jihar Jigawa, jihar da ke cikin jihohin da ambaliyar ta fi jijjigawa a bara, mutanen da ambaliyar ta shafa na cikin tsaka-mai- wuya kan yiwuwar sake fuskantar ambaliya a daminar bana.
Hakan ya biyo bayan halin ko-inkula da gwamnati ta yi kan yadda za a magance aukuwar haka a nan gaba ta hanyar samar wa ruwan hanya ko mazauni a gefe guda, a cewar mazauna yankunan da ambaliyar ta faru.
Mai magana da yawun Babban Sakataren Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Jihar Jigawa (SEMA), Habibu Yusuf Adamu Babura, ya ce tuni gwamnati ta kafa kwamati da hadin gwiwar Hukumar Kula da Kogin Hadeja-Jama’are don magance aukuwar ambaliya a nan gaba.
Habibu Babura ya ce har yanzu kwamatin na kan aiki a dam din Chalawa don tabbatar da bai kara cikowar da sai an bude shi ba. “Idan aka bude dam din ne yake haddasa ambaliya. Don haka kwamatin yana aiki a Chalawa don tabbatar da cewa ba a kara bude shi ba,” in ji Habibu Babura.
Sai dai a matakin Jihar Jigawa, Babura ya ce gwamnati na yin kokari wajen gyara duka hanyoyi da gadojin da suka lalace domin saukaka sufuri da harkokin kasuwanci.
Ya ce duk da haka gwamnatin ba ta yi kasa a gwiwa ba don ganin daminar bana ba a samu ambaliya ba.
A yankin Hadeja, mai magana da yawun Kungiyar Hadeja Ina Mafita da ke lura da kananan hukumomin Masarautar Hadeja, Amadun Kafi, ya shaida wa Aminiya cewa gwamnati ta bada tallafi amma ba a bi ka’ida ba, domin a cewarsa, mutane da dama sun yi asarar miliyoyin Naira amma wajen bada tallafi sai a ba wanda ya yi asarar Naira miliyan 10 abin da bai wuce Naira dubu 16 zuwa 17 ba.
Amadun Kafi ya ce al’ummar da ambaliyar ta shafa a Auyo da Kafin Hausa da Kaugama da Hadeja da Malam Madori da Guri sun shiga mawuacin hali duba da dimbin asarar da ta shafe su. To sai dai ya ba su shawarar su guji yin gidaje a hanyar ruwa kuma su rika kwashe magudanun ruwa domin samun sauki a yayin ambaliya.
Amadun Kafi ya ce lokaci ya kure wa gwamnati wajen tonewa da kirkirar wasu kogunan da za a dakatar da ruwan idan ya taho daga dam ko kogin Chalawa.
A yankin Dutse, Aminiya ta tattauna da wani matashi mai suna Abba Adamu Karnaya inda ya ce har yanzu gwamnati ba ta kawo ko motar sharar hanya da za a dakile ambaliyar ruwan ba.
Karnaya ya ce har yanzu suna cikin fargaba duba da yadda damina ta zo ga shi wasu da dama kara suka zagaye dakunansu suke kwana a ciki domin babu muhalli.
Ya yi kira ga gwamnati ta taimaka ta kawo wa yankin Karnaya dauki domin kada su sake shiga halin da suka shiga a bara.
A cewarsa idan suka kaura daga garin nasu yawancinsu manoma ne ina za su kai gonakinsu?
Sai dai Aminiya ta zagaya Sabon Garin Danmasara a birnin Dutse yankin da ke fuskantar ambaliyar ruwa tsawon shekaru, inda gwamnati ta yi musu magudanar ruwa babba da za ta karkatar da ruwan zuwa kogin Kudai.
A yankin Karamar Hukumar Ringim wani mazaunin garin mai suna Ibrahim IB ya ce har yanzu babu wata alamar wani aikin da ake yi na dakatar da ambaliyar ruwa a yankunan da ta auku.
IB ya ce amma gwamnatin ta yi kokari matuka wajen gyara tituna da gadojin da suka karye.
A Jihar Neja, yawancin wadanda matsalar ta shafa a garin Suleja sun ce alkawarin da hukuma ta yi masu kan sauya masu muhalli bai samu nasara ba, bayan aukuwar ambaliyar tun daga shekarar 2020.
Ambaliyar wadda ta rutsa da unguwannin Rafin-Sanyi da Kaduna Road da garin Madalla da ke Karamar Hukumar Suleja, ta yi ajalin sama da mutum 20, baya ga tarin dukiyar da ta lalata.
Ambaliyar ta fi kamari ne a Unguwan-Gwari da Unity da ke RafinSanyi a garin Suleja. Binciken Aminiya ya gano cewa, yawancin wadanda matsalar ta rutsa da su sun tashi daga gidajensu da ke gefen rafi da ya ratsa garin, in ban da kadan daga cikinsu da suka ci gaba da zama.
Malama Rukayya Adamu da ke Rafin-Sanyi na daya daga cikin wadanda ke ci gaba da zama a muhallinsu lokacin da Aminiya ta ziyarci yankin a fakon wannan mako.
Malama Rukayya wadda ta ce mijinta ya rasu shekara hudu kafin ambaliyar, ta ce a yayin ambaliyar bangaren gidansu da ya hada da shagon da take zama ya rushe, yayin da masallacin da mai gidanta ya gina da ke kusa da gidan, ya koma bangaren rafin.
Ta ce duk da cewa ba ta samun kwanciyar hankali a duk lokacin da ake yin ruwan sama tun bayan lokacin, za ta cigaba da zama a wajen a matsayin lalura kasnacewar alkawari da gwamnati ta yi na taimaka masu da wani sabon muhalli bai samu Aminiya ta zanta ta waya da wani da ya rasa ’ya’ya hudu da matarsa mai ciki a yayin ambaliyar mai suna Igbomara Thank-God, wanda ya ce hukuma ta gaza ba shi wani sabon waje kamar yadda Gwamnan Jihar Alhaji Abubakar Sani Bello ya yi alkawari a yayin ziyarar jaje.
Ya ce gidansa da hukuma ta karasa rusawa bayan ambaliyar, ya cika sharadin samun diyya kasancewar yana da takardar hukuma da ta ba da shi.
Ya ce bayan alkawarin ya yi ta bin sawu zuwa Minna Babban Birnin Jihar ba tare da nasara ba.
“A yanzu na koma yankin Abuja inda nake zaune a wajen wasu ’yan uwa tare da sake sabuwar rayuwa,” in ji shi.
Ya ce “Na rasa daukacin iyalina a yayin ambaliyar in ban da da guda wanda ba ya gidan lokacin da lamarin ya faru. Akwai kuma kadarorin da na mallaka da duk na rasa.” Mai Unguwar Unity, Malam Isa Lawan, ya yaba da aikin manyan gadoji biyu da Dan Majalisar Wakilai mai barin gado daga Suleja Alhaji Abubakar Lado ya kai yankin, ya ce sun taimaka kwarai wajen magance ambaliyar ruwa tun bayan ta lokacin.
Sa’adu Asha wanda ya rasa iyali 9 a ambaliyar Suleja ya rasu ba tare da diyyar muhalli ba Aminiya ta kuma leka Unguwar Kaduna Road, Suleja inda wani mazaunin yankin mai suna Malam Sa’adu Asha ya rasa iyali tara a yayin ambaliyar da ta gabaci ta shekarar 2020.
Wadanda ya rasa sun hada da matansa biyu da ’ya’ya bakwai. Magidancin ya koma ga Allah kamar wata biyu da su ka gabata, kamar yadda aka tabbatar a yayin ziyarar.
Wani makusancinsa mai suna Umar Faruk ya shaida wa Aminiya cewa Malam Sa’adu Asha wanda ya samu taimakon kudi daga Gwamnatin Jihar Neja ya yi sabon aure da kuma karfafa jari, sai dai bai samu zarafin sayen muhalli ba, har Allah Ya yi masa rasuwa.
Ya ce marigayin wanda ya samu karuwa daga amaryarsa ya rasu wata biyu baya bayan fama da rashin lafiya inda ya koma jiharsa ta Zamafara kuma a can ya cika.
Da yake tsokaci a kan wadanda ambaliya ta shafa a yankinsa, Dagacin Hayin Nasarawan-Iku da ke Kaduna Road, Suleja, Malam Abdulkarim Samanja ya ce yawancin wadanda ambaliyar ta shafa a yankin ba su tashi daga gidajensu ba. Ya ce hakan bai rasa nasaba da matakin da Dan Majalisar Wakilai Alhaji Abubakar Lado ya dauka na yashe rafin da ya ratsa ta yankin bayan ambaliyar.
“Kuma tun bayan aikin ba a sake fuskantar ambaliya ba saboda ruwa na wucewa cikin rafin ba tare da tsaiko ba,” in ji Dagacin.
A Jihar Sakkwato, kananan hukumomin da suka fuskanci ambaliya a bara sun hada da Goronyo da Wurno da Rabah da Wamakko da Silame da Tambuwal da Kware da Kebbe da Shagari da wasu yankunan jihar.
Shekara daya da faruwar ambaliyar da ta lakume gonaki da gidaje da dabbobi da sauran dukiyoyin jama’a abin da ya kai ga hukumomi da dama suka yi alkawarin agaza musu, ga shi wata daminar ta taho, inda suke fargabar sake komawa gidan jiya.
Nasiru Abubakar Rabah wanda ya kwashe sama da shekara 40 yana noma ya bayyana yadda ya yi asara a ambaliyar bara kuma har yanzu ba wani tallafi da aka ba su.
Ya ce. “Na yi asara sosai a ambaliyar bara ina da gona biyar, karama ita ce nake noma buhu 60 amma da aka samu ambaliyar nan buhu 10 na samu.”
Ya ce sun yi asara matuka amma daga baya Kungiyar Manoman Shinkafa ta Kasa ta zo wurinsu ta rubuta sunansu da asarar da suka yi, tun lokacin har zuwa yanzu ba wani bayani daga kowa.
Yusuf Aliyu manomi a yankin Rabah da ya ce yana da gonaki biyar ya samu ambaliya a gonakinsa ya ce duk in da yake sa ran samun buhu 80 cikin ikon Allah ya samu 10.
“A yanzu da nake magana da kai ba wani mataki da muka dauka don ba mu ne hukuma ba, kawai dai damina ta soma mun sanya kayan gonarmu.”
Ya roki Gwamnatin Tarayya ta yi masu madatsar ruwa a garin Tabanni don hakan zai sa su amfana da ruwan da ke yin ambaliya a wurarensu.
Alhaji Bala Faru sanannen manomi ne a Wamakko da Rabah, ya ce yana da gona sama da 20 da ambaliya ta sa ya rasa amfanin gona sosai.
Bala Faru ya ce ya kamata gwamnati ta gyara harkar noma in dai ana son samun ci gaba a kasar nan. Aliyu Muhammad Kebbe ya ce sun yi ambaliya sun samu asara an yi masu alkawari amma ba su ga kowa ba har yanzu ga shi damina ta dawo.
Shugaban Kungiyar Manoma ta Kasa reshen Jihar Sakkwato, Alhaji Jamilu Muhammad Sanusi ya ce an samun tallafin wucin-gadi kai-tsaye amma bayansa har yanzu ana jiran na gwamnati da ta yi alkawarin bayarwa.