Aminiya: Za mu so mu ji takaitaccen tarihinka?
Haruna NEPA: Assalamu alaikum, sunana Haruna Kassim, wanda aka fi sani da Haruna NEPA. Abin da ya sa ake mini inkiya da NEPA shi ne, tun kuruciya lokacin muna hade-haden wuta da batira da katako nan ne dai asalin sunan. Saboda a lokacin da muke harkokin ina daya daga cikin wanda ya fi iyawa. Kuma muna hada gulof ne da batir, inda muke samar da karamar fitilar hannu. Kai hatta kananan gyare-gyare da sanya soket din wuta nakan yi su ne da kaina ne. Wannan ya sa ake kirana da Haruna NEPA.
An haife ni ne a lokacin Sardaunan Sakkwato Sa Ahmadu Bello. Kusan zan iya cewa ba zan wuce shekara 50 da dan wani abu ke nan. Iyayena Kanawa ne, mutanen karamar Hukumar Garun Malam, amma ni an haife ni ne a garin Kafanchan da ke yankin Kudancin Jihar Kaduna. Na yi makarantar Arabi, amma Allah bai sa na yi makarantar boko ba.
Aminiya: Yaushe wannan lalurar ta same ka?
Haruna NEPA: Wannan lalurar ta same ni ne tun ina yaro bayan fama da ciwon bakon dauro, lokacin ban wuce shekara biyar ba.
Aminiya: Wace sana’a ka fara da ita?
Haruna NEPA: Na fara da aikin noma ne. Daga bisani sai na fara sana’ar wanki da guga. Yau kimanin shekara 23 ke nan da fara ta. Kuma ita ce sana’a daya tilo da na dogara da ita har zuwa yau.
Aminiya: Me ye ya ja hankalinka zuwa sana’ar wanki da guga?
Haruna NEPA: Na fara ne kamar wasa. Makwabta suna ba ni aiki har ta kai ga ina samun aiki daga ko ina.
Aminiya: Ta yaya kake gudanar da aikin?
Haruna NEPA: Da farko ni nake gudanar da wanki da gugar da kaina. Kuma yadda nake fahimtar kayan da nake wankewa sun fita shi ne nakan wanke sau daya, sau biyu daga nan da yardar Allah sai ka ga sun fita tas. Har ila yau, ni da kaina nake gane kaya sun fita ko kuma akasin haka. Kodayake, a yanzu nakan biya wani ne ya yi mini wankin, yayin da nake gugar da kaina.
Aminiya: Ta wace hanya kake bambance kayan mutane idan an zo karba?
Haruna NEPA: Ta wannan bangaren shi ma sai dai kawai in gode wa Ubangiji saboda da wuya ka ga na dauki kayan wani na bai wa wani. Wani abin mamaki kuma shi ne idan ma ka yi wasa kai din da ka kawo kayan, sai ka yi kuskure ka dauki na wani kana ganin naka ne. Saboda shi zai yi amfani da launin kayansa ne. Yayin da ni zan yi amfani da wurin da na ajiye kayan da kuma yanayin yadda na san kayan. Sau da yawa an sha samun irin wannan, wani zai zo ya nuna wasu kayan ya ce nasa ne, sai in ce masa a’a ba nasa ba ne. Daga nan sai ya ga na fito masa da nasa.
Aminiya: Ko an taba samun kuskure ka bai wa wani kayan wani?
Haruna NEPA: Kasan yau da kullum ba abin da ta bari. To amma dai kafin a samu irin wannan kuskuren akan dade.
Aminiya: Akwai wata dabara ce da kake amfani da ita wajen bambance kayan?
Haruna NEPA: Yanzu ka ga wanda ya kawo mini kaya yau, ka ga yana zuwa na san ina zan neme su. Har ila yau, wanda ya kawo min kaya kimanin mako guda da ya wuce na san wurin da zan neme su.
Aminiya: Ta bangaren guga ko ka taba kona kayan wani?
Haruna NEPA: Da wuya, sai dai ’yan matsalolin da ba za a rasa ba.
Aminiya: Kamar kaya nawa kake wankewa a rana?
Haruna NEPA: Idan na samu aiki sosai ina iya wanke kaya guda 50. Har ila yau, idan aka yi dace da wuta nakan fara goge wasu daga cikinsu duka a rana guda.
Aminiya: Wace fa’ida ka samu albarkacin wannan sana’ar?
Haruna NEPA: Babbar nasara dai ka ga ba na zuwa bara, ba na zuwa roko. Kuma duk wata hidima da wannan sana’ar nake gabatar da ita. Ta kai ga har na sayi fili kuma a halin yanzu na yi nisa da gini.
Aminiya: Akwai wadansu kalubale da za ka ce kana fuskanta?
Haruna NEPA: Babban kalubale shi ne rashin zaman lafiya da ake fuskanta, wanda shi ne silar dawowarmu nan garin Rido. Kuma mun dawo nan ne kimanin shekara 15 da suka wuce biyo bayan wani rikici da ya faru.
Aminiya: Kana da wani buri?
Haruna NEPA: Bai wuce fatan in kammala ginina ba, wato muhallin da zan zuba iyalina.
Aminiya: Ya batun iyali fa?
Haruna NEPA: Ina da mata daya da ’ya’ya shida.