✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Harsashin masu garkuwa da uwa ya kuskure danta

Harsashin da ya kashe dogarin Sarkin Bungudu ya kusa fasa kan yaron.

Wani karamin yaro mai shekara daya ya tsallake rijiya da baya, bayan harsashin ’yan bindagar da suka kashe dogarin Sarkin Bungudu ya kusa samun sa a kai.

A harin ne ’yan bindiga suka yi garkuwa da Sarkin Bungudu, Alhaji Hassan Attahiru, bayan sun bindige dan sandan da ke tsaron lafiyarsa, sauran kuma suka samu raunin harbi.

Yaron da mahaifiyarsa da mai aikinsu na tafiya ne a motar haya lokacin da ’yan bindiga suka kai tare motocinsu sukua bude musu wuta a hanyar Abuja zuwa Kaduna.

“’Yar aikin ta samu ta tsere, wani fasinja da ya dauki yaron kuma ya rike shi gangam ya tsere da shi; A takaice, harsashin da aka kashe dogarin sarkin da shi ya kusa fasa kan yaron,” inji wata fasinja da ke cikin motar.

A cewarta, mahaifiyar yaron ba ta da lafiya ne shi ya sa ta kasa guduwa a lokacin da aka kawo harin.

“Motarmu daya da su [yaron], kuma da rana aka kawo harin a daidai wurin da aka yi garkuwa da basaraken.

“An yi garkuwa da wata mata (mahaifiyar yaron) a motarmu, ita kuma tana tare ne da danta mai shekara daya da ’yar aikinsu,” inji ta.

Ta ce mahaifiyar yaron ce kadai aka yi garkuwa da ita a motar, sauran sun samu sun tsere.

Sanarwar da Rudunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna ta fitar kafin wayewar garin Laraba ta ce ba a tantancen adadin mutanen da masu garkuwar suka sace ba, amma wasu mutum biyu da suka samu raunuka na saum kulawa a asibiti.

Kakakin Rundunar, Mohammed Jalige ya ce, lamarin ya faru ne a daura da kauyen Dutse da ke kan babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja, kuma an tura karin jami’ai zuwa wurin domin ceto mutanen da aka yi garkuwa da su lami lafiya.

“Bayanan da muka samu sun nuna tare motocin aka yi, aka bude musu wuta babu kakkautawa sannan aka yi awon gaba da mutanen”, inji Jalige, wanda ya ce wadanda suka yi aika-aikar za su yaba wa aya zaki.