✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Harin ’yan tawayen Yemen ya yi barna a rumbun ajiye man Saudiyya a Jeddah

Harin na zuwa ne gabanin bude gasar tseren motoci ta Formula One da za a fara a Jeddah

Gobara ta tashi a wani rumbun ajiye mai na kasar Saudiyya da ke birnin Jeddah bayan ’yan tawayen Yemen na Houthi sun kaddamar da hare-hare kan kasar.

Kafafen yada labaran Saudiyya a ranar Juma’a sun rawaito cewa hayaki ya tirnike sararin samaniya bayan da wasu makaman rokoki da ’yan tawayen suka harba suka fada kan rumbunan da ke birnin na Jeddah.

Harin na zuwa ne gabanin bude gasar tseren motoci ta Formula One da za a fara yi a birnin ranar Lahadi mai zuwa.

Ko da dai kafafen yada labaran Saudiyyar da ma kamfanin man kasar ma Aramco ba su ambaci sunan wajen ba, amma bayanai na nuni da cewa an kai harin ne a ma’ajiyar da aka taba kai wa harin a ’yan kwanakin baya.

Daga bisani dai da yammacin Juma’a, kakakin Houthi, Yahya Sarea, ya ce sun kai wa ma’ajiyoyin na Aramco hari ne da makamai masu linzami, yayin da suka kai wa matatun man da ke Ras Tanura da Rabigh hari da jirage marasa matuka.

Yahya ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Juma’a cewa, “Hare-haren an kai su ne a kan wuraren kamfanin Aramco da ke biranen abokar gabarmu [Saudiyya] na Jeddah da Riyadh

Ya kuma ce sun kai wasu hare-haren kan wasu wuraren na kamfanin na Aramco a  garuruwan Jizan da Najran da Ras Tanura da kuma Rabigh.

Hare-haren dai na zuwa ne yayin da Saudiyya take ci gaba da jagorantar kawancen da ke yaki da ’yan tawayen na Houthi, wadanda suka taba kwace iko da kasar Yemen a watan Satumban 2014.