Jami’an ’yan sanda uku da ke aiki da ofishin rundunar na Maraban Jos a Jihar Kaduna sun rasa ransu bayan wani hari da ’yan bindiga suka kai yankin ranar Juma’a.
Aminiya ta gano cewa an kai harin ne da misalin karfe 11:30 na daren ranar Juma’a, inda aka harbe ’yan sandan uku.
- COVID-19: China ta tallafa wa Najeriya da rigakafi 470,000
- An ga Daliban Islamiyyar Tegina a Shiroro
Yanzu haka dai ’yan sandan na can suna samun kulawa a wani asibiti da ba a bayyana ba.
A cewar wata mazauniyar yankin, Fatima Mohammed, harin da aka kai ofishin ’yan sandan ne ya farkar da su.
“Da muka fara jin karar harbe-harbe sai muka fara kiran jami’an tsaro a waya domin ankarar da su, cikin ikon Allah ’yan bindigar ba su sami nasarar shiga yankin ba.
“A lokacin da suka shigo kuma ana yayyafi kadan-kadan, daga bisani kuma ruwa mai karfi ya tsuge, watakila dalilin kenan da ya sa suka sassauta.
“Bayan harin, mun kashe ’yan sandan da suka jikkata zuwa wani asibiti a yankin domin samun kulawa.
“An jima ana kawo wa yankinmu hari ana sace mutane da dama, ana biyan diyya a sirrance.
“Ko ana gobe Sallah, an sako wasu mata da suka shafe kwana 30 a hannun ’yan bindiga bayan an biya kudin fansa. Dalilin kenan da ya sa mutane da dama ke guduwa saboda kada a sace su,” inji Fatima.
Sai dai ta ce al’amura sun fara daidaita a yankin, yayin da mutane ke ci gaba da harkokinsu na yau da kullum.
Kakakin Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalige ya tabbatar da kai harin da kuma harbin ’yan sandan su uku.
Ko a kwana shida da suka wuce, sai da ’yan bindigar suka sace mutum bakwai, ciki har da mata uku a gundumar Anguwar Gajere da ke Karamar Hukumar Birnin Gwari ta Jihar ta Kaduna.
Sun kuma sami nasarar sace shanu guda 50 a kauyen.