✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Harin ’yan bindiga: Sojoji na bukatar N500m don katange NDA

Hakan dai na cikin rokon da ta yi yayin kare kasafin kudinta na 2022.

Makarantar Horar da Sojojin Najeriya ta NDA ta roki Kwamitin Tsaro na Majalisar Wakilai ya amince da bukatarta na kudi Naira miliyan 500 domin katange makarantar da ke Afaka a Jihar Kaduna.

Hakan dai na cikin rokon da Kwamandan makarantar, Manjo Janar IM Yusuf ya yi lokacin da yake kare kasafin kudin makarantar na 2022 a gaban majalisar ranar Laraba.

Rokon dai na zuwa ne ’yan watanni kadan bayan ’yan bindiga sun kai hari makarantar a watan Agustan 2021, inda suka fasa katangarta, sannan suka kashe jami’an soja biyu, suka sace daya.

Kwamandan ya kuma roki karin miliyan 450 don sashen jami’a na makarantar da kuma miliyan 300 don bikin yaye dalibai na shekara-shekara.

Kazalika, ya bukaci karin miliyan 200 a matsayin kudaden gudanarwa a kowanne wata don sayen dizal, man fetur, gas da sauran gyare-gyaren yau da kullum.

A jimlace dai, Kwamandan ya gabatar da bukatar Naira biliyan 17 gaban majalisar a kasafin kudin na 2022.

Manjo Janar Yusuf ya ce akwai bukatar kara kudaden gudanarwar makarantar, la’akari da tarin kalubale da yawan bukatunta.

Da yake nasa jawabin, Shugaban kwamitin, Hon. Babajimi Benson ya yi alkawarin cewa za su duba bukatar kara yawan kudaden don a ba su damar aikin horar da sojoji yadda ya kamata.