Ana fargabar mutuwar mutum takwas yayin da ’yan bindiga suka kai hari wasu Kananan Hukumomi uku a Jihar Kaduna da ke Arewacin Najeriya.
Kananan Hukumomin da harin ’yan bindigar ya shafa sun hada da Giwa, inda aka kashe mutum uku, sai kuma Igabi wacce aka kashe mutum hudu a cikinta yayin da kuma aka kashe mutum daya a Chikun.
- ‘Mutanen Najeriya za su yaba wa Buhari a karshen mulkinsa’
- Real Madrid ta kammala daukar David Alaba
Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar, Samuel Aruwan, ya tabbatar da faruwar lamarin cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a.
A cewarsa, harin da aka kai Karamar Hukumar Igabi ya auku ne a kauyukan Dakayauro da Sabon Birni inda rayukan mutum hudu suka salwanta yayin da kuma aka sace shanu kimanin 25.
Kwamishinan ya tabbatar da jikkatar mutum biyu yayin harin da aka Karamar Hukumar Igabi, inda kuma aka kashe wani jagoran al’umma, Dauda Adamu a Unguwar Ayaba.
Kazalika, ya ce ’yan bindigar sun kuma kutsa wasu gonaki a Kauyen Gigani da ke yankin Kerawa a Karamar Hukumar Igabi, inda suka yi awon gaba da manyan shanu 14 da ake hudar gona da su.
Ya ce Gwamna Nasir El-Rufa’i yana mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan wadanda suka rasa ’yan uwansu sakamakon harin tare da addu’ar Mai Duka Ya jikansu.