Akalla mutane 22 suka mutu a wani hari da ake kyautata zaton ’yan ta’adda da kaddamarwa kan wasu kauyuka da ke yammacin Nijar kan iyakar kasar da Mali.
Wasu majiyoyin sun shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP a jiya Litinin cewa, wasu ne mayaka dauke da muggan makamai suka farwa kauyen Motogatta da ke jihar Tillaberi yankin da ya hada iyakokin kasashen Nijar Mali da kuma Burkina Faso.
A cewar wasu shaidun gani da ido, cikin mutanen 22 da suka mutu a harin har jami’na tsaron sa kai da ke bayar da tsaro ga al’ummar kauyen.
Yankin na Tilaberri na sahun yankunan Jamhuriyyar Nijar da kef ama da matsalolin tsaro tsawon shekaru, musamman daga kungiyoyin da ke ikirarin jihadi.
- Ana shirin tsige Ganduje daga shugabancin APC
- Mali da Burkina Faso sun mika wa ECOWAS wasikar ficewarsu
Matsalolin tsaro na ci gaba da ta’azzara a yankin Sahel duk kuwa da yadda Sojoji suka kwace mulki daga hannun gwamnatocin fararen hula a kasashe 3 mafiya fama da matsalar ta ta’addanci da suka kunshi Nijar da Mali da kuma Burkina Faso.
A ranar 17 ga watan Disamban bara, Janar Abdourahamane Tiani ya bayyana cewa matsalolin tsaro sun kau a kasar bayan nasarar gwamnatin Sojin na murkushe barazanarsu.