✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Harin Sojin Najeriya kan ’yan bindiga ya yi kuskuren kashe yara 7 a Nijar

Sun yi kuskuren kisan yaran ne a kokarin farmakar ’yan bindiga.

Wani hari na fatattakar ’yan bindiga da Sojin saman Najeriya suka kai ya yi kuskuren hallaka kananan yara 7 tare da jikkata wasu 5 a kauyukan iyakar kasar da Nijar.

Gwamna Jihar Maradin Chaibu Abubakar ya ce harin wanda dakarun Najeriya suka kai bisa kuskure kan zaton cewar ’yan fashi daji ne, ya faru a garin Nachade da ke a yankin Madarounfa da ke kan iyaka da Najeriya.

A cewar gwamnan lamarin ya faru ne a kauyen Nachade inda ya shafi mutane 12 kuma tuni bakwai daga ciki wadanda dukkaninsu kananan yara ne suka mutu yayinda 5 ke karbar kulawar gaggawa.

Gwamna Aboubacar da ya ziyarci kaburburan yaran da aka binne a ranar Asabar da kuma wurin da harin ya faru, ya yi amanna cewa dakarun na Najeriya sun yi kuskuren kai harin kan kananan yaran da ke wasa a yayin da iyayensu ke halartar wani biki a kauyen Nachade.

Yankunan da dama da ke cikin Jihar Maradin wadanda ke kan iyaka da Najeriya na fuskantar hare-haren ’yan bindiga da ke kwararowa daga Jihohin Katsina, Sakkwato da kuma Zamfara.

Har zuwa yanzu dai babu sanarwa daga rundunar Sojin Najeriya kan farmakin.

%d bloggers like this: