✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Harin Saudiyya ya kashe sama da mutum 70 a Yemen

Saudiyya ta kai harin ne wani gidan yarin da ke birnin Saada, hedkwatar Houthi a Yemen.

Akalla mutum sama da 70 ne aka halla, wasu 138 kuma suka jikkata a wani hari da dakarun Saudiyya suka kai kan wani gidan yari da ke Arewacin kasar, kamar yadda kungiyar ba da agaji ta Medecins Sans Frontieres (MSF) ta tabbatar.

Lamarin dai ya dada ta’azzara rikicin da ake fama da shi tsakanin kasar ta Saudiyya da mayakan Houthi na kasar Yemen.

Saudiyya dai ta tsananta kai hare-hare a kan ’yan tawayen kasar, ’yan kwanaki kadan bayan ’yan Houthi sun lakada wa wani mai shiga tsakani na Hadaddiyar Daular Larabawa duka ranar Litinin, sannan suka harba makamai zuwa cikin Saudiyyan.

Wasu hotunan bidiyo da mayakan na Houthi suka fitar ranar Juma’a sun nuna ma’aikatan jinkai suna kokarin tono gawarwaki daga cikin baraguzai sakamakon harin.

Kakakin MSF, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa an halaka mutum akalla 70 sannan aka jikkata wasu kimanin 138.

Ya ce an tattara alkaluman ne daga wani asibiti da ke birnin Saada, inda ya ce wasu asibitocin kuma na ci gaba da karbar wasu, a daidai lokacin da aikin ceto ke ci gaba da gudana.

Sai dai kakakin kungiyar bayar da agaji ta Red Cross a kasar ta Yemen, Basheer Omar, ya ce adadin mutanen zai ci gaba da karuwa a birnin na Saada, wanda shi ne ke zama kamar hedkwatar Houthi.

“Akwai mutum sama da 100 da aka kashe ko aka jikkata, adadin na ci gaba da karuwa,” inji Basheer, inda ya ambato alkaluman da ake ci gaba da tattarawa daga asibitocin birnin na Saada da gudunmawar Red Cross din.