Rundunar ’Yan Sandan Jihar Neja ta tabbatar da mutuwar mutum uku a harin da ’yan bindiga suka kai Masarautar Kagara da ke Karamar Hukumar Rafi ta jihar.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Neja, Monday Kurya, shi ne ya bayyana hakan ga Kamfanin Dillacin Labarai Najeriya (NAN) a garin Minna a ranar Laraba.
- DSS ta kama wadanda suka yi wa daliba fyade har ta mutu
- Najeriya A Yau: Tsarabar Zamfara: ‘Da Shiga Jihar Za Ka Ga Damuwa’
Kurya ya ce harin ya faru ne da misalin karfe 5:30 na yammacin ranar Talata, inda mahara sama da 100 suka farmaki masarautar tare da ofishin ’yan sanda da ke yankin.
Ya kara da cewa wani dan sanda da wasu mutum biyu sun rasu a sakamakon harin ’yan bindigar.
A wani labarin kuma, Kwamishinan ’Yan Sandan ya ce wasu mahara sun kai hari kauyen Kachiwe da ke Karamar Hukumar Munya ta Jihar.
Ya ce maharan sun fito daga maboyarsu da ke Jihar Kaduna sannan suka kai harin.
Amma ya ce, “Ba ni da cikakken bayanin adadin mutanen da suka mutu a yayin harin.”
Har wa yau, ya ce ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen ci gaba da yakar ta’addanci a jihar, inda ya roki al’umma da su ci gaba da taimakon ’yan sanda da bayanai da suka dace.
A cewarsa tuni aka fara gudanar da bincike don gano wadanda suka kai harin don a kamo su sannan a hukunta su kamar yadda doka ta tanadar.
Ya ce an tura ’yan sanda yankin don su kare rayuka da dukiyoyin al’umma a yankin.