✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Harin Mafa: Gwamnatin Yobe Ta Tallafa Wa Iyalan Mamata

An raba kudaden ne ga iyalai 128 da suka rasa rayukansu

Gwamnatin Jihar Yobe ta raba tallafin kudi ga iyalan wadanda harin kungiyar ISWAP ya rutsa da su a garin Mafa da ke Ƙaramar Hukumar Tarmuwa a kwanakin baya.

Alhaji Mala Misty, mai baiwa gwamna Mai Mala Buni shawara kan harkokin ilimi mai zurfi ne ya bayyana hakan a ranar Laraba a Damaturu.

Gwamnan wanda mataimakinsa  Idi Barde Gubana ya wakilta, tun baya ya ambata bayar da gudunmawar Naira miliyan 30 domin tallafa wa iyalan wadanda abin ya shafa, baya ga gudunmawar da sauran masu jajantawa suka bayar.

An raba kudaden ne ga iyalai 128 da suka rasa rayukansu da kuma wadanda harin ya raba da muhallansu, domin rage tasirin lamarin.

Daga cikin wadanda suka ci gajiyar tallafin da suka hada da Malama A’isha Danbade da Malam Mustapha Muhammad sun mika godiyarsu ga gwamnan da sauran masu jajantawa da goyon bayansu.

Harin na ISWAP ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama tare da raba wasu da dama da muhallin su.