Gwamnatin Jihar Neja ta ba da umarnin bude daukacin makarantun gwamnatin da ta rufe bayan an yi garkuwa da daliban makarantar sakandaren GSC Kagara a Jihar.
Kwamishinar Ilimi ta Jihar Neja, Hannatu Salihu ce ta sanar da haka bayan kusan wata biyu da rufe marakantun bayan harin Makarantar Kagara.
- Abba Kyari ya fara farautar wadanda suka kai wa Ortom hari
- Gobara ta tashi a kusa da Masallacin Annabi na Madina
- Guguwa ce ta sa na ‘samu juna biyu’ —Mace
- Tinubu ya ziyarci Sarkin Kano, zai gana da sarakuna
“Dukkannin makarantun gwamnati za su ci gaba da darusa ranar 29 ga Maris, 2021. Makarantun kwana da ke cikin birane kuma ranar 6 ga Afrilu, 2021,” inji sanarwar da ta fitar.
Ta kara da cewa, “Makarantun kwana da ke kauyuka marasa hadari sosai kuma za su koma a matsayin na je-ka-ka-dawo daga ranar 6 ga Afrilu, 2021.
“Wadanda ke wurare masu hadari sosai kuma da za a koma gudanar da su a dunkule kuma, sai nan gaba za a sanar da ranar bude su bayan daukar cikakkun matakan tsaro.
“Daliban da ke makarantun kwana a wasu wurare wadanda yanzu za su koma na je-ka-ka-dawo kuma za a mayar da su makarantun garuruwannsu.”
Bayan garkuwa da daliban Makarantar Kagara da ’yan bindiga suka yi da dalibai 27 da kuma ma’aikata da iyalansu, gwamnatin Jihar ta rufe makarantun kwanan da ke jihar.
Daga baya masu garkuwar sun sako su a ranar 27 ga watan Fabrairu, bayan kwana 17 a hannunsu a cikin dajin da suka kai su, tun ranar 10 ga watan da suka yi awon gaba da su.
Bayan kwanaki kuma, gwamantin ta ba da umarnin rufe ragowar makarantun, domin ba wa hukumomin taro damar gudanar da bincike da kuma fito da tsarin tabbatar da tsaro a makarantu.