✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Harin jirgin kasa: Yadda jami’an tsaro suka gaza daukar mataki duk da bayanan sirri

Bayanan sirri sun nuna yadda 'yan bindiga suka jima suna dakon harin jirgin kasa.

Jami’an tsaro sun gaza dakile harin da ’yan bindiga suka kai kan wani jirgin kasa da ya taso daga Abuja zuwa Kaduna a ranar Litinin, duk da samun bayanan sirri daga hukumomin tsaro.

Harin da aka kai kan jirgin kasan, mai dauke da fasinjoji sama da 300, shi ne hari mafi muni da aka taba kai wa kan wani jirgin kasa a Najeriya.

Akalla gawarwakin mutum tara aka tsinto daga inda harin ya faru a ranar Talata, yayin da wasu sama da 20 suka samu raunuka sakamakon harbi da kuma turmutsutsu, kana kuma ’yan bindigar suka yi awon gaba da fasinjoji da dama.

Manyan jami’an tsaro sun bayyana wa Aminiya a ranar Laraba cewar, wasu bayanan sirri sun nuna yadda ’yan bindiga suka jima suna kokarin farmakar jirgin kasa, kuma sun yi gargadi kan daukar mataki amma aka yi burus da su.

Baya ga gazawar da jami’an tsaro suka yi na dakile harin, Aminiya ta gano cewa kwamitin tsaro na Jihar Kaduna da shugabannin runduna ta daya ta dakarun sojin Najeriya, sun bukaci Hukumar Kula da Jiragen Kasa ta Najeriya (NRC) da ta dakatar da jigilar fasinja cikin dare.

Sai dai NRC ta yi watsi da umarnin da hukumomin tsaron suka ba ta kan irin hatsarin da ke tattare da yin hakan.

Manajan Daraktan NRC, Injiniya Fidet Okhiria ya tabbatar da cewa an aike wa da hukumar takarda kan ta daina tashin jirgin kasa da yamma.

“Sun aike mana takarda cewa suna fargabar cewa ’yan bindiga za su iya kai hari amma wannan a watan Disamba zuwa Janairu ne. Amma mun sanar da su cewar in har hakan gaskiya ne bai kamata a daina tashin jirgi ba, kamata ya yi a nemo mafita.

“Kuma ba ma yin jigilar dare. Jirgi na karshe da ke tashi a kullum da yamma ya ke tashi ya isa bayan duhu ya yi.

“Mun yi imanin idan muka dakatar da zirga-zirgar jiragen kasa, hakan na nufin ’yan ta’adda sun yi nasara ke nan.

“Yawancin jiragen kasa na samun jami’an tsaron da ke musu rakiya daga rundunar ’yan sanda,” a cewarsa.

Harin da ’yan bindigar suka kai kan jirgin kasan ya fusata dimbin ’yan Najeriya, inda wasu da dama ke ganin gwamnatin da ke cewa gwamnati ta gaza cika alkawuran da ta dauka yayin yakin neman a zabeta.