Tun bayan da aka samu rahoto cewa jirgin kasa ya taka bam a Kaduna, ’yan Najeriya da dama suka shiga kafofin sadarwa na zamani suna tsokaci a kan lamarin.
Daga cikin wadanda suka wallafa sakonnin har da wadanda abin ya rutsa da su, da kuma wadanda lamarin ya shafi ’yan uwa da abokan arzikinsu.
Daya daga cikin sakonnin da aka wallafa a shafin Twitter da ya yi tashe shi ne na wata matashiya mai suna Chinelo Megafu Nwando ta rubuta, “Ina cikin jirgin, kuma an harbe ni. Don Allah ku yi min addu’a”.
A shafin nata dai, Chinelo ta rubuta cewa ita likitar hakori ce, tana aiki da Asibitin St. Gerald dake Kaduna.
Sai dai sa’o’i kadan bayan ta wallafa sakon nata, sai wani wanda ya ce shi abokin aikinta ne ya yi tsokaci da cewa ta riga mu gidan gaskiya a asibitin da aka kai ta.
Wannan tsokaci na abokin aikin Chinelo ya jawo ce-ce-ku-ce, inda wasu ma’abota shafin na Twitter suka nuna shakku game da lamarin suna cewa wasa ne, wasu kuma suke tausaya mata.
Amma duk ba wannan ba – abin da ake magana a kan ya faru da Chinelo abu ne da ya faru da mutane da dama.
An harbe su yayin harin amma suka cika a asibiti, wasu ma ba su karasa asibitin ba, a hanya suka cika.
Mutane da dama sun wallafa sakonni da yawa a shafukansu game da iyalansu da abokansu da suke asibiti da wandanda suka rasa rayukansu.
Misali, wani mai suna Bashir Usman ya wallafa wani sako da yake cewa, “Muna sanar da rasuwar wani dan uwa [tsohon dalibin] GSCS Abdu Isa Kofar Mata a harin da aka kai kan jirgin kasa a Kaduna a daren [Litinin]…”
Akwai wasu kuma wadanda ’yan uwa da abokan arziki suka sanar da rasuwarsu a shafukan na sada zumunta, amma daga bisani aka gano ba su mutu ba.
Alal misali, an bayar da labarin cewa Muhammad Amin Mahmood, dan takarar kujerar Shugaban Matasa na APC daga yankin Arewa maso Yamma yana cikin wadanda ’yan bindiga suka harbe.
Amma daga bisani ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa ya samu rauni ne daga harbin bindiga kuma yana samun kulawa a asibiti.
Komai na iya faruwa a irin wannan yanayi, kuma zai yi kyau kafin mutane su fara yada mutuwar wani su bari a kamala bincike a tabbatar.
A yanzu dai ’yan Najeriya sun zuba ido su ga sanarwar da hukumomi za su fitar mai dauke da cikakkun bayanan mutanen da abin ya shafa.