Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya bai wa iyalan mutum tara da suka rasu a harin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna kyautar Naira miliyan 18.
A ranar 28 ga watan Maris 2022, ’yan bindiga suka farmaki jirgin kasan da ya taso daga Abuja zuwa Kaduna dauke da fasinjoji 362.
- Rasha ta yi gwajin wani ‘hatsabibin’ makami mai linzami
- Maharan sun harbe shugabannin PDP biyu a Filato
A harin mutum tara suka rasu yayin da wasu 26 suka ji raunuka, sai kuma wasu da ’yan bindigar suka sace, wadanda zuwa yanzu ba a san adadinsu ba.
Wata sanarwa da Sakataren Hukumar Bada Agajin Gaggawa na Jihar (KADESMA), Muhammed Mkaddas, ya fitar, ta ce za a bai wa iyalan kowane mamaci kyautar miliyan biyu.
Kazalika, Mukaddas ya ce za a bai wa kowane daga cikin mutum 22 wadanda suka ji rauni kyautar N250,000.
Har wa yau, ya ce daga cikin fasinjoji 369, mutum 264 ne suka amsa kiran gwamnatin jihar kan tallafa musu game da lafiyarsu.
Kazalika, ya ce hukumar ta kafa wata kwamiti da za ta rika karbar bayanai daga iyalan wadanda aka sace a harin.