✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Harin Isra’ila Ya Tilasta Rufe Asibitin Gaza

Wani jami'in kiwon lafiya na Falasdin ya ce an rufe asibitin Kuwaiti da ke birnin Rafah a Gaza.

Wani jami’in kiwon lafiya na Falasdin ya ce an rufe asibitin Kuwaiti da ke birnin Rafah a Zirin Gaza.

Jami’in ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin. Ya ce, an rufe asibitin ne sakamakon hare haren da Isra’ila ke ci gaba da kai wa birnin.

Asibitin Kuwaiti na daga cikin asibitoci biyu da ke aiki a birnin Rafah da ke kudancin Gaza.

Suhaib Al-Hams, daraktan asibitin ya ce “Muna sanar da rufe asibitin kwararru na Kuwaiti, kuma ma’aikatan lafiyarmu za su koma filin karbar magani da ake shiryawa a kusa da nan.”

Kamfanin Dillacin Labaran Najeriya (NAN) ya bayyana cewa sanarwar ta ce, hukumar asibitin ta ce,  akwai alamun cewa sojin Isra’ila na kai hare-hare da gangan a yankin asibitin a kwanan nan.

A halin da ake ciki kuma, Asibitin Al-Aqsa da ke Deir al-Balah, a tsakiyar Zirin Gaza, ya yi gargadin cewa idan sojojin Isra’ila suka ci gaba da hana kai masa man fetur to dole zai dakatar da aiki.

Sanarwar da asibitin na cewa tun ranar Lahadin da ta gabata sojojin Isra’ila ke hana samar da man fetur da ake amfani da shi wurin samar da lantarki a asibitin.

Sanarwar ta kara da cewa, asibitin na kula da lafiyar sama da mutane 1,200 da wasu da suka ji rauni.

Sun ce a cikin asibitin a halin da ake ciki akwai majinyata 600 da ke fama da ciwon koda da ke bukatar wankin koda.

Sanarwar ta yi kira ga kasashen duniya da su matsa wa Isra’ila lamba ta samar da lita 50,000 na man fetur domin tabbatar da aikin kiwon lafiya na tsawon kwanaki 10 masu zuwa.