✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Harin Imo: An girke jami’an tsaro don kare Hausawa

An girke jami'an tsaro a yankin Hausawa don gudun abin da ka iya zuwa ya dawo

Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodimma, ya aike da jami’an tsaro 40 don kare Ama Awusa, yankin da Hausawa suka fi yawa a Owerri, babban birnin Jihar.

Hadimin gwamnan na musamman kan harkokin jinsi, Sulaiman Ibrahim Sulaiman ne ya bayyana haka cikin wata tattaunawarsa da wakilinmu a ranar Juma’a.

“Daga Allah muke kuma gare Shi za mu koma. Wadansu daga cikinmu sun kai shekara 150 suna rayuwa a nan, don haka, muna kallon kanmu ’yan asalin wannan yankin babu maganar wariya,” inji shi.

Sulaiman, wanda shi ne Ggarkuwan Hausa a Jihar, ya ce an wayar da kan al’ummar kan kaunar zaman lafiya a tsakaninsu.

Da yake karin haske kan harin da ’yan bindiga suka kai Hedikwatar ’Yan Sandan Jihar, Suleiman ya jaddada kalaman Gwamna Uzodinma cewar ’yan siyasa ne suka dauki nauyin harin.

Ya ce jama’ar yankin ba su dauki kisan wani mahauci da aka yi ba a matsayin wata hanya ta tayar da fitina ba, face kaddara.

Kazalika, ya musanta zargin cewar masu rajin kafa kasar Biyafara ne suka kai harin, inda ya ce har yanzu ba a gano wadanda suka kai harin ba.

Sulaiman, ya ja kunnen wasu da suke barazana ga rayuwar ’yan kabilar Igbo a yankin Arewa, da cewar kada su biye wa wanda ba su son zaman Najeriya a lafiya.

Ya bayyana Imo a matsayin Jiha mai cikakken zaman lafiyar da dan Arewa zai iya rayuwa a cikinta.