✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Harin GSSS Kankara: An rufe makarantun kwanan Jihar Katsina

Iyayen dalibai sun yi wa Gwamna Aminu Masari ihu a lokacin da ya ziyarci makarantar

Gwamnan Katsina Aminu Masari ya rufe daukacin makarantun kwanan da ke jihar bayan ’yan bindiga sun kai hari inda ake zargi sun yi garkuwa da dalibai a makarantar sakandaren GSSS Kankara.

Umarnin nasa na zuwa ne bayan ya ziyarci makarantar domin ganin da abin ya faru, inda ya yi arba da iyayen dalibai da suka taru domin sanin halin da ’ya’yansu suke ciki.

Majiyarmu ta ce fusatatuun iyayen daliban sun yi wa gwamnan ihu  a lokacin da ya nemi yi musu bayani.

Ganau sun ce sai da jami’an tsaron gwamnan suka harba hayaki mai sa hawaye kafin tawagarsa ta iya barin wurin.

A sanarwar da kakakinsa, Abdu Labaran, Masari ya ba wa iyayen daliban hakuri da kuma tabbacin jami’an tsaro sun riga sun fara aikin ceto yaran daga hannun ’yan bindiga.

Ya ce a lokacin ziyarar, Masari ya yi zama da hukumomin tsaro, sarakuna da wasu daga cikin iyayen daliban inda ya ba su baki ya bukaci a kwantar da hankali jami’an tsaro za su kubutar da yaran.

Abdu Labaran ya ce gwamnatin jihar da ta tarayya na yin dukkan mai yiwuwa domin kawar da ayyukan ’yan bindida da sauran manyan laifuka a jihar.

 

Dalibai nawa suka bace?

Kwamishinan Ilimin Jihar Katsina, ya ce kawo yanzu an gano dalibai 404 a makarantar yayin da daliban da suka tsere bayan harin ’yan bindigar ke ta dawowa.

Farfesa Badamasi Lawal ya ce kimanin dalibai 800 ne a makarantar sadda abin ya faru, kasancewar ’yan ajin fita sun riga suka kammala jarabawa sun koma gida.

A cikin dare ne dai mahara kimanin 100 dauke da muggan makamai suka yi wa GSSS Kankara dirar mikiya inda suka yi dauki ba dadi tsakaninsu da jami’an ’yan sandan da ke tsaron makarantar kwanar.

Kawo yanzu ba a kai ga tantance ko maharan sun yi garkuwa da dalibai ba, da kuma adadin daliban ba.

 

Matsalar tsaro a Jihar Katsina

Jihar Katsina ce mahaifar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, kuma  ta yi kaurin suna wurin ayyukan ’yan bindiga  masu garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa.

’Yan bindigar sun kashe daruruwan mutane, sun yi wa mata da kanan yara fyade, baya ga miliyoyin Naira da suka yi fashi, ko suka karba a matsayin kudin fansa daga iyalai.

Ayyukan ta’addancin ’yan bindiga a jihar, kamar takwarorinta yankin Arewa maso Yamma, sun kona kauyuka tare da tilasta wa mazauna da manoma kaura.

Harin na faruwa ne a sa’o’i kadan bayan Shugaba Buhari ya fara ziyarar mako guda a mahaifarsa, Daura, da ke jihar.

Kawo yanzu dai babu wani kwakkwarar sanarwa daga Fadar Shugaban Kasa game da harin na Kankara.

Mutane daga sassan jihar sun sha yin zanga-zangar neman a kawo karshen matsalar, da kuma bukatar masari da Buhari su yi murabus saboda sun gaza magance matsalar.

A baya Masari ya amsa gazawarsa game da shawo kan matsalar, yayin da Gwamnatin Tarayya ta kafa babban sansanin soja domin magance matsalar.

A nasa bangaren Buhari ya sha nanata bayar da tabbataci da kuma umarni ga sojoji na ganin karshen matsalar.