Dakarun sojin Najeriya sun aika mayakan Boko Haram 21 lahira bayan kungiyar ta kai hari a garin Geidam na Jihar Yobe dab da shan ruwa a ranar Juma’a.
Mayakan sun bakunci lahira ne bayan sojoji sun yi musu luguden wuta ta sama da kasa, jim kadan da shigarsu garin na Geidam, mahaifar mukaddashin Shugaban ’Yan Sandan Najeriya.
- Sojoji sun kama makamai a fadar sarakunan Binuwai
- Buhari ya girgiza da rasuwar mahaifiyar Sarkin Kano
- Buhari ya girgiza da rasuwar mahaifiyar Sarkin Kano
Kakakin Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya, Birgediya Mohammed Yerima, ya ce sojojin Rundunar ‘Operation Tura Takaibango’ sun kuma kwato muggan makamai daga hannun ’yan ta’addan.
Ya ce bayan maharan sun lalata turakun sadarwa sun fasa shaguna suna satar kaya ne suka gamu da gamonsu a hannun sojin kasa da da jiragen yakin da suka fatattaki ’yan ta’addan, suka kashe 21 daga cikinsu.
“Hazikan dakarun sun kwato motar yaki dauke da bindigar harbo jirgi; bindigar AK 47 guda takwas, rokoki da gurneti-gurneti da kwanson albarusai.
“Sauran su hada da: dubban harsasai, bindigar harba gurneti, na’urar tayar da abun fashewa, wayoyin sadarwar oba-oba da na salula, akwatunan kanikanci, da sauransu,” inji sanarwar.
Yerima ya kara da cewa sojojin suna ci gaba da sharar yankin domin ganowa da kuma karasa ragowar ’yan ta’addar, wadanda yawancinsu sun tsere ne da raunukan harbi a jikinsu.
Sai dai ya ce sojoji uku sun samu rauni a yayin fadan da aka gwabza, amma suna murmurewa a asibitin sojin da ake jinyar su.
Yerima ya ambato Shugaban Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya, Laftanar-Janar Ibrahim Attahiru, yana jinjina wa namijin kokarin sojojin tare da bukatar su da su kara zage damste wajen ganin bayan ayyukan ta’addanci a yankin.